Siyasar Najeriya
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kaduna ta ce ta kammala duk wasu shirye-shirye na gudanar da zaɓen kananan hukumomi a ranar 19 ga watan Oktoba, 2024.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya umurci shugabannin rikon kwarya na kananan hukumomi 18 da kansilolin gundumomi 33 na jihar da su kama aiki.
Tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osobo ya bayyana yadda ya yi mu'amala da tsohon shugaban soji a Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a 1985.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya bayyana cewa bai taɓa ɗaukar ko Naira daga kason kuɗin kananan hukumomin jihar da aka tƴro daga tarayya ba.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar da Gwamna Hope Uzodinma ya samu a zaben gwamnan jihar Imo. Ta yi watsi da karar da jam'iyyun adawa suka shigar.
Matan jam'iyyar PDP sun yi zazzafan zanga zanga a birnin tarayya Abuja suna bukatar a dakatar da shugabar mata ta kasa saboda nuna wariya a shugabancin jam'iyya.
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya yi kira ga ƴan Najeriya su jingine duk wani banbanci a halin yanzu, su goy bayan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zabe ta bayyana zaben dan majalisar tarayya na Yabi da Shagari a matsayin wanda bai kammalu ba, ta umarci INEC ta ƙarisa zaɓe.
Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi maraba da sauya sheƙar tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, ya ce APC ta ƙara karfi a Kudu.
Siyasar Najeriya
Samu kari