Ganduje Ya Samu Matsala a APC Yayin da Tsohon Kwamishina Ya Fice Daga Jam'iyyar, Ya Fadi Dalili

Ganduje Ya Samu Matsala a APC Yayin da Tsohon Kwamishina Ya Fice Daga Jam'iyyar, Ya Fadi Dalili

  • A yanzu haka dai masana harkokin siyasa na kallon diramar da ke faruwa a siyasar jihar Edo kasancewar komai ya rincaɓe a jam'iyyar PDP mai mulki da APC
  • Yayin da Obaseki da mataimakinsa ke takun-saƙa kan wanda zai zama gwamna, ita ma jam’iyyar APC na fama da rikicin cikin gida kan wanda zai ɗaga tutar jam’iyyar a zaɓen gwamnan jihar mai zuwa
  • Na baya-bayan nan shi ne tsohon kwamishina, Andrew Emwanta, wanda ya fice daga APC saboda dambarwar da ta faru a zaɓen fidda gwanin da aka gudanar a ranar Asabar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Bayan kammala zaɓen fidda gwani na gwamna, tsohon kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama’a na jihar Edo, Andrew Emwanta, ya fice daga jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Ganduje ya shiga babbar matsala yayin da matasan APC suka ɓalle da zanga-zanga kan abu 1

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, tsohon kwamishinan ya yi murabus ne saboda kura-kuran da aka samu a zaɓen fidda gwani na gwamna da aka gudanar a ranar Asabar, 17 ga watan Fabrairu.

Emwanta ya fice daga APC
Emwanta bai gamsu da yadda APC ta gudanar da zaben fidda gwani ba a Edo Hoto: Andrew Emwanta
Asali: Facebook

Ku tuna cewa zaɓen fidda gwanin da aka yi a ranar Asabar ya samar da mutum uku da suka yi nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwanin, Gwamna Hope Uzodimma ya sanar da Dennis Idahosa a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Jami’in zaɓen fidda gwani, Dr. Stanley Ugboajah, ya bayyana Sanata Monday Okpebolo a matsayin zaɓaɓɓen ɗan takarar jam’iyyar APC tare da bayyana Okpebolo a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Haka kuma, Ojo Babatunde, wanda ya yi iƙirarin cewa shi ne wakilin jami’an zaɓen a dukkan ƙananan hukumomin ya bayyana Anamero Dekeri a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Meyasa Emwanta ya fice daga jam'iyyar APC?

Kara karanta wannan

Wa ya isa ya ja da mu? Wike ya cika baki, ya aike da sako mai zafi ga gwamnan PDP

A wata wasiƙa da ya aike wa shugaban gunduma ta 7, ƙaramar hukumar Egor kuma aka raba wa manema labarai a ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu, Emwanta ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar.

Wani ɓangare na wasiƙar na cewa:

"Na rubuto ne domin in miƙa takardar yin murabus daga jam’iyyar APC, daga yau 18, ga watan Fabrairu, 2024.
"Shawarar da na yi na ficewa daga jam’iyyar ya samo asali ne daga rashin bin tsarin dimokuraɗiyyar cikin gida, sakamakon kura-kuran tsarin zaɓen fidda gwani na gwamnan Edo da aka kammala. Hakan ya sa na rasa ƙwarin gwiwa kan tsarin shugabancin jam’iyyar."

Ize-Iyamu Ya Janye Daga Takara a Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa fasto Osagie Ize-Iyamu ƴa janye daga takarar gwamnan jihar Edo a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.

Malamin addinin ya bayyana cewa ya yanke wannan shawarar ne bayan ya tattauna da iyalansa, abokansa da abokansa na siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel