Zaben 2027: Tsohon Jigo a PDP Ƴa Fadi Dalilai 3 da Za Su Sanya Atiku Ba Zai Daina Tsayawa Takara Ba

Zaben 2027: Tsohon Jigo a PDP Ƴa Fadi Dalilai 3 da Za Su Sanya Atiku Ba Zai Daina Tsayawa Takara Ba

  • Wani tsohon jigo a jam’iyyar PDP a Abuja, Deji Adeyanju, ya ce Alhaji Atiku Abubakar ba zai daina tsayawa takarar shugabancin Najeriya ba
  • Adeyanju, wanda wasu suka amince da shi a matsayin sabon daraktan yaɗa labarai na jam’iyyar PDP a lokacin wa’adin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na farko, ya ce Atiku yana da girman kai fiye da ƙima
  • Adeyanju ya bayyana cewa sha’awar “tattara kuɗi duk bayan shekara huɗu” ba za ta bari Atiku ya haƙura ba kan burinsa na shugabancin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Deji Adeyanju, tsohon ɗan jam’iyyar PDP, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ba zai daina tsayawa takarar shugaban ƙasa ba.

Kara karanta wannan

Mai ajiyar kudin jam'iyyar adawa da aka dakatar ta yi sabuwar fallasa kan shugaban jam'iyya

Kalaman Adeyanju na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke sa ran zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Atiku ba zai daina tsayawa takara ba
Deji Adeyanju ya lissafo dalilan da za su sanya Atiku ba zai daina tsayawa takara ba Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku shine ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2019 da 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi takarar shugabancin Najeriya sau shida bai yi nasara ba: a shekarun 1993, 2007, 2011, 2015, 2019, da 2023.

Kwanan nan, sansaninsa ya ce ba zai yi ritaya daga siyasar Najeriya ba, kuma zai tsaya takara a zaɓen 2027 a lokacin da ya cika shekaru 80.

Meyasa Atiku ba zai daina tsayawa takara ba?

Adeyanju ya bayyana cewa Atiku yana da haɗama, yana da girman kai fiye da ƙima, kuma yana son ƙarin kuɗi, dalilan da ba za su sanya ya ja da baya ba kan takararsa ta shugaban ƙasa.

Adejanyu ya bayyana hakan ne dai a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a daren ranar Lahadi, 18 ga watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jigon PDP ya bayyana wanda za a dorawa alhakin yunwa da wahalar da ake ciki a kasa

A kalamansa:

"Atiku ba zai daina tsayawa takara ba saboda haɗama, yawan girman kai da kuma yin takara ya zama MMM (salon damfara) nasa, yana amfani da takara wajen karbar kuɗi duk bayan shekara huɗu."

Dalilai uku, a cewar Adeyanju:

1. Atiku yana da yawan girman kai.

2. Atiku ya cika haɗama.

3. Yin takara ya zama MMM (salon damfara) na Atiku.

Bode George Ya Shawarci Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar Bode George ƴa shawarci Atiku Abubakar da ya haƙura da sake neman shugabancin Najeriya.

Bode George ya bayyana cewa ya kamata Atiku ya matsa gefe ya zama uba a jam'iyyar domin barin masu jini a jika su jaraba sa'arsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel