Mai Ajiyar Kudin Jam'iyyar Adawa da Aka Dakatar Ta Yi Sabuwar Fallasa Kan Shugaban Jam'iyya

Mai Ajiyar Kudin Jam'iyyar Adawa da Aka Dakatar Ta Yi Sabuwar Fallasa Kan Shugaban Jam'iyya

  • Rikicin cikin gida da ya dabaibaye babbar jam'iyyar adawa ta biyu a Najeriya, Labour Party ya ƙara ɗaukar zafi
  • A wannan karon, Oluchi Oparah, mai ajiyar kuɗi ta jam’iyyar da aka dakatar, ta buƙaci Julius Abure, shugaban jam’iyyar da ya bayar da cikakken bayani kan gudunmawar da aka samu daga ƙasashen waje
  • Duk da haka, Abure a wata hira ya ci gaba da cewa Opara ta jajirce ne kawai wajen "ɓata sunansa" a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mai ajiyar kuɗi ta jam’iyyar Labour Party ta ƙasa da aka dakatar, Misis Oluchi Oparah, ta ƙalubalanci shugaban jam’iyyar na ƙasa, Julius Abure kan zargin karkatar da kuɗaɗe a babban zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Tsohon jigo a PDP ya fadi dalilai 3 da za su sanya Atiku ba zai daina tsayawa

Ma'ajiyar kudi ta LP ta bukaci Abure ya bada bayani
Opara tana zargin Abure ya wawure kudaden jam'iyyar Hoto: Julius Abure, Oluchi Opara
Asali: Facebook

Ana zargin Abure da karkatar da kuɗaɗen LP

Oparah ta buƙaci Abure da ya yi bayani kan gudunmawar da aka samu daga ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje a lokacin ziyarar yaƙin neman zaɓen fan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi a ƙasar Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku tuna cewa shugabancin jam’iyyar LP ya aikewa Opara takardar dakatarwa ta tsawon watanni shida a ranar Laraba 14 ga watan Fabrairun 2024, cewar rahoton Leadership.

Hakan ya biyo bayan da Opara ta ƙalubalanci Abure a ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu, inda ta buƙaci ya yi bayani kan naira biliyan 3.5 da aka samu daga sayar da fom ɗin tsayawa takara da kuma ayyukan tara kuɗaɗe domin tunkarar zaɓen 2023.

LP ta kare Julius Abure

LP ta musanta iƙirarin mallakar Naira biliyan 3.5 tare da bayyana cewa Abure bai karkatar da kuɗaɗen jam’iyyar ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bukaci ayi abu 1 don kawo karshen matsalar tsaro

Ba tare da ja da baya kan zarginta ba, Opara, a wata hira da jaridar Punch, a ranar Lahadi, 18 ga watan Fabrairu, ta buƙaci Abure da ya ba da bayani kan kuɗaɗen da aka tara a ziyarar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na LP a Amurka.

A kalamanta:

"Haka kuma, tsawon watanni 10 zuwa 11, Abure ne kaɗai ke cire kuɗin. Ban san yadda yake yi ba, ko ta hanyar sa hannun bogi ko wasu hanyoyi."

Da yake mayar da martani kan iƙirarin na Opara, Abure ya musanta aikata laifin, yana mai cewa ma'ajin kuɗin da aka dakatar tana neman ɓata masa suna ne kawai.

Ɗan Takarar Gwamna Na LP Ya Fice Daga Jam'iyyar

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamnan jihar Edo a jam’iyyar LP, Dakta Azehme Azena ya watsar da jam’iyyarsa ana daf da gudanar da zaɓe.

Ɗan takarar gwamnan ya yi nuni rashin jin daɗinsa kan abin da bayyana rashin adalci da aka yi masa da magoya bayansaa a jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng