Babbar Magana: Ƴan Sanda Sun Bayyana Mummunan Laifin da Ya Sa Aka Kama Shugaban LP Na Ƙasa

Babbar Magana: Ƴan Sanda Sun Bayyana Mummunan Laifin da Ya Sa Aka Kama Shugaban LP Na Ƙasa

  • Ƴan sanda sun bayyana cewa an kama shugaban jam'iyyar LP na ƙasa, Julius Abure, bisa zargin yunkurin kisan kai da mallakar makamai
  • Mai magana da yawun ƴan sanda na shiyya ta 5, Tijani Momoh, ya ce wani mutumi ne ya shigar da ƙorafi kan Abure da wasu mutum huɗu
  • Ya ce har yanzu ƴan sanda na kan bincike kan zargin, inda ya tabbatar da cewa sun kama Abure tare da sauran waɗanda ake zargi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rundunar ƴan sanda ta ce ta cafke shugaban Labour Party na ƙasa, Julius Abure, ne bisa zargin yunƙurin kisan kai, mallakar bindigu da bisa ƙa'ida ba da laifuka masu alaƙa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama shugaban jam'iyya na ƙasa kan muhimmin abu, bayanai sun fito

Mai magana da yawun ƴan sanda na shiyya ta 5, Tijani Momoh, shi ne ya bayyana haka yayin hirada manema labarai yau Laraba, Channels tv ta rahoto.

Yan sanda sun faɗi dalilin kama Abure.
Mun kama Abure ne bisa tuhumar yunƙurin kisan kai - Yan sanda Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Ya tabbatar da cewa ƴan sanda sun yi ram da Abure da yammacin ranar Laraba a Benin City, babban birnin jihar Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Momoh ya yi bayanin cewa ƴan sanda sun damƙe Abure da wasu mutum huɗu biyo bayan wani ƙorafi da aka shigar kansu.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, kakakin ƴan sandan ya ce:

"Ina mai tabbatar da cewa mun kama shugaban tsagi ɗaya na jam’iyyar Labour Party (LP), Julius Abure da wasu mutane hudu.
"Hakan ya samo asali ne daga wnai ƙorafi da AIG na shiyya ta 5 ya amince da shi daga ofishin Sufeto Janar na ‘yan sanda."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kashim Shettima Ya Fadi Abu 1 da Tinubu ke yi wanda zai faranta ran 'yan Najeriya

Meyasa aka kama shugaban LP na kasa?

Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa ana tuhumar Abure da yunkurin kisan kai. Ya ci gaba da cewa:

"Akwai faifan bidiyo, sautin murya na yadda ake cin zarafin wanda ya shigar da ƙorafin, ana dukansa lokacin da ya dawo gida a bara domin gudanar da harkokin gundumomi..
"A taƙaice wannan kes ne na yunkurin kisan kai, hada baki, mallakar makamai ba bisa ka'ida ba da sauran laifuka masu alaka da waɗannan.
"Sun kuma mallaki bindigogi, ƙaramar bindiga da harsashi guda uku. Muna ci gaba da bincike. Yau aka kama su, za a fitar da cikakken bayani nan gaba."

A wani rahoton kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Kwankwaso, ya samu nasara a kotu kan dakatarwan da aka masa.

Babbar kotun jihar Kano ta kuma hana wasu jiga-jigan NNPP daga bayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyya na rikon kwarya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel