Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Fice Daga PDP, Ya Faɗi Jam'iyyar da Ya Koma Saboda Abu 1

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Fice Daga PDP, Ya Faɗi Jam'iyyar da Ya Koma Saboda Abu 1

  • Jam'iyyar PDP ta rasa tsohon mataimamin kakakin majalisar dokokin jihar Abia, Ifeanyi Uchendu, wanda ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC
  • Jigon siyasar ya bayyana cewa ya zaɓi shiga APC ne domin yana da burin ɗaga siyasarsa zuwa matakin ƙasa
  • A cewarsa, matsawarsa zuwa kasa zai bai wa matasa masu tasowa dama domin tauraruwar su ta haska a siyasa kuma su bada gudummuwa a jihar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Abia wanda ya sauka kwanan nan, Ifeanyi Uchendu, ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Uchendu, wanda ya fito daga gundumar Isiama, ya yi aiki a majalisar dokokin jihar Abia ta 7 kuma ya wakilci mazaɓar Ohafia ta kudu, kamar yadda The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya samu babban mukami, kungiyar AU ta ba shi nauyi a nahiyar Afrika

Babban jigon PDP ya koma APC.
Tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Abia ya fice daga PDP zuwa APC Hoto: Official APC, PDP
Asali: Twitter

Jigon siyasar shi ne shugaban sashin midiya da yaɗa labarai kuma mai magana da yawun majalisar dokokin jihar Abia da ke Kudu maso Gabas, rahoton Daily Post.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 24 ga watan Mayun 2017 tsohon mataimakin shugaban majalisar ya koma PDP daga jam’iyyar APGA, inda aka zabe shi a matsayin mai wakiltar Ohafia ta Kudu a majalisar dokokin Abia ta 6.

Meyasa ya zaɓi komawa APC maimakon LP mai mulki?

Da yake tsokaci kan dalilin shiga APC maimakon Labour Party mai mulkin jihar Abia da kuma tasirin da zai iya yi a sabuwar jam'iyyar, Mista Uchendu ya ce:

"APC jam'iyya ce ta ƙasa kuma ita ke mulkin Najeriya, idan baku manta ba na nemi takara domin wakiltar mutane na a majalisar tarayya. Yanzu ina kokarin maida hankali a siyasar ƙasa ne.

Kara karanta wannan

"Ya dauki nauyin kawunnai na 10 zuwa Hajji": Tambuwal ya tuna haduwarsu ta karshe da Wigwe

"Lokaci ya yi da zan matsa zuwa matakin siyasa ta ƙasa saboda ina da yaƙinin muna da isassun mutanen da zasu bada duk gudummawar da ake buƙata a amatakin jiha.
"Hakan kuma zai taimaka wa wasu su samu damar tasowa a sansu a siyasa tun daga tushe kafin su kai ga matakinmu.”

Matasan APC sun ɓalle da zanga-zanga a Edo

A wani rahoton kuma Awanni bayan kammala zaɓen fidda gwani, matasan APC a jihar Edo sun gudanar da zanga-zangar adawa da shugabannin jam'iyya.

Sun yi kira ga uwar jam'iyya ta ƙasa karkashin Ganduje ta rushe kwamitin gudanarwa (SWC) na jihar wanda Jarret Tenebe ke shugabanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel