Wa Ya Isa Ya Ja da Mu? Wike Ya Cika Baki, Ya Aike da Sako Mai Zafi Ga Gwamnan PDP

Wa Ya Isa Ya Ja da Mu? Wike Ya Cika Baki, Ya Aike da Sako Mai Zafi Ga Gwamnan PDP

  • Tsohon gwamnan Rivers kuma ministan babban birnin tarayya na yanzu, Nyesom Wike, ya aike da saƙo ga magajinsa, Siminalayi Fubara
  • Wike, a wani taron coci da aka yi a ranar Lahadi, ya yi taƙama da cewa shi da ƴan sansaninsa za su yi nasara a zaɓen 2027 saboda ƙawancen da ke tsakanin PDP da APC a jihar
  • Ku tuna cewa Wike da Fubara sun kasance ubangida da yaronsa a siyasance, amma su biyun sun rabu watanni shida bayan Fubara ya zama gwamna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Port Harcourt, jihar Rivers - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, a wani saƙo da ya lulluɓe ga gwamna Siminalayi Fubara na Rivers, ya yi alfahari da cewa shi da tawagarsa ba za su yi rashin nasara ba a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Mai tsaron gidan Ivory Coast ya yi amfani da laya a wasan karshe na AFCON 2023

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce ƙawancen da sansaninsa ya gina zai sa zaɓen 2027 ya zama mai sauƙi a wajensa, cewar rahoton jaridar Channels tv.

Wike ya aike da sako ga Fubara
Dangantaka ta yi tsami tsakanin Wike da Gwamna Fubara Hoto: Siminalayi Fubara, Nyesom Wike
Asali: Twitter

Wike yayi burga kan zaɓen 2027

Ministan ya bayyana shirinsa na babban zaɓe mai zuwa a wajen wani taron coci na Sanata Barinada Mpigi, a Koroma cikin ƙaramar hukumar Tai ta jihar a ranar Lahadi, 18 ga watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Tare da ƙarfin da muke da shi, ban san wani wanda zai iya ƙalubalantar mu ba. Zan iya gaya muku kamar gobe ne 2027. A gare ni, har yanzu yana da nisa. Ba zan iya jira ba.
"Shugabannin jam’iyyun guda biyu, APC suna nan, da PDP. A ina za ku samu irin wannan haɗin kan? Wacce jiha? A cikin Rivers ne kawai za ku iya samun wannan haɗin kan."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu da gwamnoni sun fara shirin ɗaukar mataki 1 da zai magance matsalar tsaro a Najeriya

Shin Wike da Fubara sun ƙare rigima?

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa mutane da dama ba su ji daɗin kawancen siyasa da shi da ƴan adawa suka ƙulla a jihar ba, suka yi ƙoƙarin raba su, ya ƙara da cewa “mun ƙi mu rabu".

Ku tuna cewa Wike ya zaɓi Fubara tare da tabbatar da ganin ya gaje shi a matsayin gwamnan jihar.

Sai dai kuma, bayan watanni shida da hawan Fubara kan mulki, sai ya rabu da ubangidansa da aka sani a siyasance, kuma su biyun sun daga nan dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu.

Karanta wasu labaran kan Wike

"Shi ba dan jihar nan ba ne": Wike ya bayar da karin haske kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Kotu ta yi hukunci kan sahihancin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Wike da Gwamna Fubara

Gwamnan PDP ya aike da muhimmin sako ga Wike da Tinubu bayan nasara a Kotun Koli

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi da sauran fitattun 'yan Najeriyan da suka rasu a hatsarin jirgin sama

Ƴan Sanda Sun Sheƙe Ɗan Daba a Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an ƴan sandan jihar Rivers sun halaka wani riƙaƙƙen shugaban ƴan daba da ake nema ruwa a jallo a jihar.

2Baba wanda a kwanakin baya ya halaka wani DPO na ƴan sanda ya gamu da ajalinsa ne bayan ƴan sandan sun kai samame a maɓoyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel