Siyasar Najeriya
Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin mutum 10 wanda zai sa ido tare da tabbatar da an bi umarnin kotun ƙoli na ba kananan hukumomi ƴancin cin ganshin kai.
Jam'iyyar NNPP ta sanar da kudaden da masu sha'awar tsayawa takara a zaben kananan hukumomin jihar Kano za su biya. NNPP ta sanya N600,000 a kujerar Ciyaman.
Kungiyar matasa masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku sun ce babu wani mahaluki da zai iya dakatar da Atiku a zaben shugaban kasa na 2027.
Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo ya amince da naɗin mutane 1,192 a matsayin masu taimaka masa na musamman, matakin zai fara aiki a watan Satumba.
Wani babban jigon APC, Kwamared Abdulhakeem Adegoke Alawuje ya yi hasashdn cewa ƴan Najeriya ba za su gujewa Tinubu ba a zaben shugaban ƙasa na 2027.
Shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya musanta raɗe-raɗin takarar shugaban ƙasa a 2027, ya ce wasu ne ke son haɗa shi faɗa da Bola Tinubu.
Ana raba ayyukan mazabu ga yan majalisun kasar nan 109 domin gudanar da ayyukan ci gaba a sassa daban-daban na mazabunsu ciki har da Barau Jibrin da Ali Ndume.
Tsohon mai ba Rabi'u Musa Kwankwaso shawara kuma dan majalisar wakilai ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC. Sanata Barau Jibrin ne ya karbe su a Abuja.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta musanta batun cewa akwai shirin tsige Abdullahi Umar Ganduje daga mukamin shugabanta na kasa. Ta ce ba gaskiya ba ne.
Siyasar Najeriya
Samu kari