Rikicin Jihar Plateau: Fulani Na Zargin Sojojin Najeriya da Yi Masu Bakin Aika-Aikata

Rikicin Jihar Plateau: Fulani Na Zargin Sojojin Najeriya da Yi Masu Bakin Aika-Aikata

  • Wasu al'ummar Fulani a jihar Plateau sun koka kan yadda sojoji suka yi masu barna ana zaune kalau a kauyensu
  • Sun ce an kashe masu shanu tare da kone duk wasu kadarori da suka mallaka a yankin da ke Arewa ta Tsakiya
  • Mazauna sun bayyana kukansu, sun nemi a yi bincike don daukar matakan da suka dace na doka kamar yadda aka tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Plateau - A jiya ne al’ummar Luggere da ke karamar hukumar Barkin Ladi ta Jihar Plateau, suka zargi jami’an sojin ‘Operation Safe Haven’ a yankin da kone gidajensu da motoci da sauran kadarorinsu.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji 17: Tinubu ya fusata, ya ba da sabon umarni ga dattawa da sarakunan Okuama

Sun kuma zargi jami’an tsaron da bude wuta kan shanunsu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar da dama daga cikinsu.

Fulani na zargin sojoji da ja masu asara a Plateau
Fulani na zargin sojoji da kashe masu dabbobi a Plateau | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Hakazalika, sun zargi an lalata msu duk wasu muhimman kayayyakin amfanin yau da kullum ciki har da rijiyar burtsatse.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka farmaki kauyen Fulani

Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne biyo bayan kisan da aka yi wa wani soja a wani wurin hakar ma’adinai a unguwar Shurun da ke gundumar Ropp a karamar hukumar Barkin Ladi.

A cewarsu, sojoji sun fara harbe-harbe ta sama kafin daga bisani su kona gidajensu da sauran kayayakinsu, inda suka ce da yawa daga cikinsu sun gudu daga yankin, rahoton Daily Trust.

Shaida daga bakin wani mazaunin yankin

Bala Salihu, wani mazaunin yankin da aka kone gidansa ya ce:

“Muna tsaka da barci sojoji suka isa yankin. Sun kona gidaje da ababen hawanmu kan laifin da ba mu aikata ba.

Kara karanta wannan

Mahara sun farmaki dalibai mata a Jami'ar Tarayya da ke Arewa, sun tafka barna

“Wurin hakar ma’adinai da aka kashe sojan ya yi nesa da matsuguninmu. Akwai ma al'ummomi biyu kusa da wurin hakar ma'adinai kafin namu. Babu wata shaida da ke nuna cewa wanda ya kashe sojan ya fito ne daga yankinmu.
“Ba mu taba fuskantar irin wannan ta’asa ba a baya. A farkon watan nan an kashe mana shanu, yanzu haka an kona mana gidaje da dukiyoyinmu.
"Lokacin da aka kashe shanunmu sama da 100, jami’an tsaro ne suka roke mu da mu yi hakuri. Me jami’an tsaro suke so mu yi? Ba su gudanar da wani bincike ba kafin matakin suka dauka.”

Ana bincike, inji sojojin Najeriya

Uthman Abdullahi, wani mazaunin yankin ya ce sun yi asarar miliyoyin nairori sakamakon farmakin, kuma ya yi kira da a gudanar da bincike.

Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Samson Zhakom, da aka tuntuba kan lamarin, ya yi alkawarin gudanar da bincike tare da fitar da rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an tsaro da bincike 5 da aka taɓa tuhuma kan saɓa doka

Jihar Plateau dai na daga jihohin Arewacin Najeriya da ake yawan samun sabani tsakanin kabilu da ma jami'an tsaro.

Rikici ya barke tsakanin makiyaya da manoma

A wani labarin kuma, mutane da dama sun halaka sannan an kona gidaje da dama a wata fadar da ta barke tsakanin makiyaya da manoma a kauyen Tumbi, karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rikicin ya fara ne ranar Juma'a, sannan har ya zuwa lokacin kammala hadin wannan rahoton ana ci gaba da fafatawa tsakanin ɓangarorin biyu.

Wani mazaunin kauyen mai suna Ibrahim Musa ya bayyana cewa daruruwan mutane sun tsere daga kauyen, sannan ya ce an kona gidaje sama da guda dari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel