Yaron El-Rufai Ya Maidawa Uba Sani Martani Masu Nauyi Kan Batun Bashin jihar Kaduna

Yaron El-Rufai Ya Maidawa Uba Sani Martani Masu Nauyi Kan Batun Bashin jihar Kaduna

  • Uba Sani ya tada kura da ya zargi gwamnatin baya da cin makudan bashin da ya bar jihar Kaduna a mawuyacin hali
  • Bashir El-Rufai ya yi amfani da dandalin X da aka fi sani da Twitter, ya caccaki gwamnatin da APC ta ke jagoranta
  • Yaron tsohon gwamnan ya nuna gwamnatin Uba Sani ba ta san inda ta dosa ba, tana fakewa da nauyin biya bashi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Wasu suna ganin an fara sharan fagen rikicin siyasa a jihar Kaduna tun da gwamna Uba Sani ya fara wasu maganganu.

A ranar Asabar aka rahoto Mai girma Uba Sani ya na kokawa game da tulin bashin da mai gidansa, Malam Nasir El-Rufai ya bar masa.

Kara karanta wannan

"Na samu bashin $587m, N85bn", Uba Sani ya tona yadda El-Rufai ya bar Kaduna

Bashir El-Rufai
Bashir El-Rufai ya soki gwamnatin Uba Sani Hoto: Senator Uba Sani/Bashir El-Rufai
Asali: Facebook

Bashir El-Rufai v Gwamna Uba Sani

Jim kadan bayan gwamna ya yi wannan magana ne sai aka ji yaron tsohon gwamna, Bashir El-Rufai ya maida martani a dandalin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Leadership ta rahoto, Bashir El-Rufai ya rika yin wasu shagube da ake zargi gwamnatin Uba Sani yake maidawa martani.

A kokarinsa na kare gwamnatin baya wanda mahaifinsa ya jagoranta, Bashir ya nuna cin bashi ba laifi ba ne, ko Legas ta na da bashi.

Kaduna: Yaron El-Rufai ya yi maganganu

Wannan Bawan Allah ya zargi gwamnoni da gaza tabuka abin komai illa canza kason da ake ba su daga asusun FAAC zuwa Daloli.

Bashir El-Rufai bai tsaya a nan ba, ko da bai kama sunaye ba, ya tuhumi gwamnati da rashin sanin inda ta dosa wajen gudanar da aikinta.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya magantu kan naɗa ɗan Kwankwaso a matsayin kwamishina

Me Bashir El-Rufai ya fada a X?

"Wadannan mutane sun fahimci ba su iya komai kuma yadda za su boye wannan shirme shi ne su saki layi."
"Tun daga Gwamnan da kullum yan barci a Abuja zuwa tulin tarkacen hadiman da aka nada saboda sakaryar manufar siyasa kurum."

- Bashir El-Rufai

Uba Sani ya karbowa El-Rufai bashi

Baro-baro aka ga Bashir El-Rufai yana tunawa duniya gwamna mai-ci ne ya shiga ya fita har aka amincewa Kaduna ta karbo aron kudi.

Yaron tsohon Ministan ya jawo abin magana a shafin nasa da ya ce ana kashe N7bn a gina dakin taro a lokacin ana kukan babu kudi.

"Shi ne Sanata daga Kaduna da ya lallaba kuma ya amince da bashin nan."
"Gwamnati mai-ci a Kaduna tana gina dakin taron N7bn kuma ta na kukan bashin da tsohuwar gwamnati ta bar mata."

- Bashir El-Rufai

Kara karanta wannan

A wurin buɗa baki da manyan Malamai, Gwamnan APC ya rage farashin shinkafa da kashi 50

Ayyukan Gwamna Uba Sani a Kaduna

Ana da labari Malam Uba Sani ya ɗauki nauyin karatun ɗaliban Kuriga da aka ceto daga hannun ƴan bindiga a makon da ya wuce.

Gwamnan na jihar Kaduna ya kuma ba da kyautar N10m ga iyalan malaminsu da ya mutu a hannun masu garkuwa da mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel