Bola Tinubu Ya Ɗauko Ɗan Arewa, Ya Naɗa Shi a Babban Muƙami a Watan Azumi

Bola Tinubu Ya Ɗauko Ɗan Arewa, Ya Naɗa Shi a Babban Muƙami a Watan Azumi

  • Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Dakta Abdullahi Bello a matsayin sabon shugaban hukumar ɗa'ar ma'aikata ta ƙasa (CCB)
  • Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana haka a a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, 2024
  • Ya ce shugaban ƙasar na fatan Dakta Bello zai yi amfani da gogewarsa wajen tabbatar da ɗabi'u masu kyau tsakanin ma'aikatan gwamnati

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Dakta Abdullahi Bello a matsayin shugaban hukumar da’ar ma’aikata (CCB) ta ƙasa.

Wannan naɗi da shugaba Tinubu ya yi zai tabbata ne idan har majalisar dattawa ta tantance shi tare da tabbatar da shi a muƙamin.

Kara karanta wannan

Yayin da Tinubu ya halarci jana'izar sojoji, hadiminsa ya soki Buhari kan rashin kulawa

Bola Ahmed Tinubu.
Dakta Bello ya zama sabon shugaban CCB Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wannan na nufin Dakta Bello ya gaji Farfesa Isah Mohammed, wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a watan Nuwamba 2018.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, shi ne ya tabbatar da naɗin Bello a matsayin shugaban CCB a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 28 ga watan Maris.

CCB: Tinubu ya yaba da ƙwarewar Bello

Ya bayyana Bello a matsayin kwararre kuma wanda ake sa ran zai yi amfani da gogewarsa wajen jagorantar hukumar ta samu nasarar aiwatar da ayyukanta yadda ya kamata.

Babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta na zamani ya wallafa wannan sanarwa a shafinsa na manhajar X wadda aka fi sani da Twitter.

"Dakta Bello kwararren ne wanda ya shafe sama da shekaru 25 yana aiki a ɓangarori daban-daban da suka haɗa da harkokin banki, tabbatar da doka, hada-hadar kudi, da koyarwa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnan PDP ya naɗa tsohon shugaban tsageru a matsayin Sarki mai martaba

"Shugaban ƙasa yana fatan sabon shugaban, bayan majalisar dattawa ta tabbatar da shi, zai jagoranci hukumar cikin gaskiya da kiyaye ɗa'ar ma'aikata wajen gudanar da harkokin gwamnati.
"Da kuma tabbatar da cewa ayyuka da halayen jami’an gwamnati sun dace da mafi kyawawan ɗabi’u da riƙon amana."

- Cewar Ajuri Ngelale.

Uba Sani ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai

A wani rahoton na daban Malam Uba Sani ya ɗauki nauyin karatun ɗaliban makarantar Kuriga da aka ceto daga hannun ƴan bindiga ƙarƙashin gidauniyarsa.

Gwamnan Kaduna ya kuma ɗauki alkawarin sabunta makarantar firamare da sakandiren gwamnati da ke Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel