Gwamnan APC Ya Yi Magana Kan Batun Taso Ganduje a Gaba Sai Ya Yi Murabus

Gwamnan APC Ya Yi Magana Kan Batun Taso Ganduje a Gaba Sai Ya Yi Murabus

  • Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia, ya mayar da martani kan kiraye-kirayen da aka ce yana yi na Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus
  • Alia, a wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Mista Tersoo Kula, ya fitar, ya bayyana hakan a matsayin zuƙi ta malle, yana mai cewa yana da kyakkyawar alaƙa da shugaban na jam’iyyar APC na ƙasa
  • Gwamnan ya bayyana cewa babu wani lokaci da ya taɓa cewa Ganduje ya yi murabus, inda ya ƙara da cewa yana goyon bayan shugabancin Ganduje na APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Makurdi, jihar Benuwai - Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya yi kira ga Alhaji Abdullahi Umar Ganduje shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya yi murabus.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da matar Gwamnan PDP bayan musayar wuta? Gaskiya ta bayyana

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 27 ga watan Maris a Makurdi, babban birnin jihar ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Tersoo Kula.

Gwamna Alia ya kansa kan batun murabus din Ganduje
Gwamna Hyacinth Alia ya musanta cewa ya nemi Ganduje ya yi murabus Hoto: Benue State Government, Dr. Abdullahi Umar Ganduje - OFR
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa sakataran na mayar da martani ne kan rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai suka yaɗa cewa gwamnan ya buƙaci shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya yi murabus.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje: Me Gwamna ya ce kan murabus?

Tersoo Kula ya ce babu wani lokaci da gwamnan ya taɓa neman shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya yi murabus.

Ya ƙara da cewa Gwamna Alia yana da kyakkyawar alaƙa da shugabannin APC ƙarƙashin jagorancin Ganduje.

A kalamansa:

"Ya zama wajibi a fayyace cewa ko kaɗan Gwamna Alia bai taɓa shirya, halarta, ya aika da wakili ko shiga duk wani taro domin tattauna batun tsige ko kiran murabus ɗin Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ba."

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Buhari ya fadi yadda gwamnatin Tinubu za ta yi nasara

Ya ce gwamnan ya mayar da hankali ne wajen ganin an samu canji mai kyau a jihar Benuwai, rahoton jaridar Daily Post ya tabbatar.

Kula ya ƙara da cewa:

"Yana nan a tsaye bisa nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na shugaban jam’iyyar APC a jihar Benuwai kuma yana yin duk abin da ya dace domin shirya samun nasarar jam’iyyar a nan gaba."

Ganduje: Jihar da APC za ta ƙwace

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam'iyyar za ta karɓe mulkin jihar Anambra daga hannun jam'iyyar APGA.

Ganduje ya yi nuni da cewa APGA ta kasa samar da ci gaban da ake buƙata a jihar wanda hakan ya sa take tafiyar hawainiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel