INEC Ta Jero Sunayen Jam'iyyun Siyasa 19 da Za Su Fafata a Zaben Gwamnan Jihar Ondo

INEC Ta Jero Sunayen Jam'iyyun Siyasa 19 da Za Su Fafata a Zaben Gwamnan Jihar Ondo

  • Hukumar INEC ta bayyana cewa jam'iyyun siyasa 19 ne suka nuna sha'awar shiga zaben gwamnan jihar Ondo da za a yi a watan Nuwamba, 2024
  • Kwamishinar INEC ta jihar, Misis Oluwatoyin Babalola, ta gana da wakilan jam'iyyun a Akure, babban birnin jihar ranar Jumu'a
  • Ta kuma jero sunayen jam'iyyun tare da gargaɗinsu kan bin dokoki da ƙa'idoji yayin zaben fitar da gwani a wata mai zuwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce jam’iyyun siyasa 19 ne za su fafata a zaben gwamnan jihar Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba.

Kwamishinar zaɓe ta jihar, Misis Oluwatoyin Babalola, ce ta bayyana hakan yayin ganawa da wakilan jam'iyyun siyasa a Akure ranar Jumu'a, 29 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ya faɗawa manyan Malamai da Sarakuna a wurin buɗa baki a Aso Villa

Shugaban INEC, Mahmud Yakubu.
INEC ta jero sunayen jam'iyyun da za su shiga zaben Ondo Hoto: INECNigeria
Asali: Twitter

Yayin da take jawabi a wurin taron, Babalola ta bayyana cewa jam'iyyun sun nuna sha'awar za su tsayar da ƴan takara a zaben gwamna mai zuwa, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce jam’iyyun sun kuma sanar da hukumar zaɓe game da zaɓen fidda ɗan takarar gwamna, wanda zai wakilci kowace jam'iyya a zaɓen.

Kwamishinar INEC ɗin ta buƙaci jam'iyyun su bi dokoki da ƙa'idojin da ke ƙunshe a cikin kundin tsarin mulkinsu yayin zaben fitar da gwani a wata mai zuwa.

Haka zalika ta shawarce su da su tabbatar an gudanar da zabubbukan na farko cikin lumana, kwanciyar hankali, da gaskiya domin tabbatar da sahihancin sakamakon, rahoton Guardian.

Zaben Ondo: Jerin jam'iyyun siyasa 16

Kwamishinar ta bayyana sunayen jam'iyyun, ga su kamar haka:

1. All Progressives Congress (APC)

Kara karanta wannan

Jam'iyyar adawa ta faɗi wanda za ta ba tikitin takara domin ya kayar da Tinubu a 2027

2. Peoples Democratic Party (PDP)

3. Accord Party

4. Action Alliance (AA)

5. African Action Congress (AAC)

6. African Democratic Congress (ADC)

7. African Democratic Party (ADP)

8. All Progressives Grand Alliance (APGA).

9. Allied Peoples Movement (APM)

10. Action Peoples Party (APP)

11. Boot Party

12. Labour Party (LP)

13. New Nigeria Peoples Party (NNPP)

14. National Rescue Movement (NRM)

15. Peoples Redemption Party (PRP)

16. Social Democratic Party (SDP)

17. Youth Party (YP)

18. Young Progressives Party (YPP)

19. Zenith Labour Party (ZLP).

Sanata Ningi zai koma kujerarsa

A wani rahoton kuma Sanata Godswill Akpabio ya ce nan ba da daɗewa ba majalisar dattawa za ta ɗage dakatarwar da ta yi wa Sanata Abdul Ningi.

Shugaban majalisar ya bayyana haka ne yayin da yake hira da ƴan jarida jim kaɗan bayan ya dawo Najeriya daga wurin taro a ƙasar Switzerland.

Asali: Legit.ng

Online view pixel