Siyasar Najeriya
Wasu manyan jiga-jigan NNPP da PDP tare da ɗaruruwan mambobi a Kawo Kaduna, sun fice daga jam'iyyunsu zuwa APC mai mulki saboda nasarorin Malam Uba Sani.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce ba za ta janye karar da ta shigar kan Godswill Akpabio ba, yayin da a hannu daya wasu ke zarginta da siyasantar da lamarin.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya fadi tasirin da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke da shi ga APC da kuma amfanin da zai yi a 2027.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya tabo batun wanda zai gaje shi a kujerar gwamnan jihar. Ya nuna cewa ba shi da hurumin yanke wannan hukuncin.
APC ta samu ƙaruwa da tsohuwar ƴar takarar mataimakiyar gwamna a inuwar PDP, Dr Emana Ambrose-Amawhe ta sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki a Kuros Riba.
Fubara ya dawo daga hutun makonni biyu, bayan ya gana da Tinubu a Landan. An ce gwamnan da aka dakatar ya kuma gana da Wike, ya durkusa har gwiwa yana neman gafara.
Fitaccen mawakin nan, Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara ya sako sabuwar waƙar da ya yi wa Tinubu a wurin liyafar da aka shiryawa shugaban ƙasa.
Kungiyar ta Afenifere ta yi magana kan zaben 2027 inda ta bayyana goyon bayanta ga shugaban kasa, Bola Tinubu ya kammala shekaru takwas a mulkin kasa.
Yayin da Remi Tinubu ke gudanar da shirin tallafawa mata, wasu sun fita daga wajen taron tallafa musu da ake yi karkashin matar shugaban kasa a Port Harcourt.
Siyasar Najeriya
Samu kari