2027: Umarnin da Aka ba Ministocin Tinubu daga Arewa kan Yan Adawa Kafin Zabe

2027: Umarnin da Aka ba Ministocin Tinubu daga Arewa kan Yan Adawa Kafin Zabe

  • Wasu ministocin Arewa sun fara fitowa fili don kare gwamnatin Bola Tinubu daga sukar da ‘yan adawa da wasu manyan ‘yan siyasa ke yi masa
  • Tuni wasu majiyoyi suka ce an ba ministocin umarnin yin duk abin da ya dace domin kare mai gidansu daga zage-zagen yan adawa
  • Wasu jiga-jigan siyasa daga Arewa suna takun saka kan inda shugabancin APC zai koma bayan 2027, yayin da ake fafutukar kara karfin Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Wasu ministocin Arewa a gwamnatin Bola Tinubu sun fara fitowa fili don nuna goyon bayansu ga gwamnatinsa.

Ministocin sun dauki wannan mataki ne duba da yadda yan adawa ke sukar gwamnatin ba kakkautawa.

An taso ministoci a gaba domin kare gwamnatin Tinubu
Ministocin Bola Tinubu daga Arewa sun fara mayar da martani kan sukar gwamnati da yan adawa ke yi. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

Umarnin gwamnatin Tinubu ga ministoci daga Arewa

Punch ta lura da yadda wasu ministoci da manyan jami’an gwamnati suka fara mayar da martani kan sukar da ake yi wa gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya gana da tsohon gwamnan APC, an yi hasashen shirin tumbuke Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da sukar ‘yan adawa ke kara karfi, majiya mai tushe ta ce fadar shugaban kasa ta umurci ministoci da ‘yan siyasa su mayar da martani.

Wani na kusa da ministocin tsaro a majalisar Tinubu ya ce an ba shugabannin Arewa umarni su kalubalanci adawa da ke karuwa kan Shugaban kasa.

Ministoci sun fito domin kare Tinubu

Majiyar ta ce:

"Ina da tabbacin cewa kwanan nan, kun ga da yawa daga cikin ministocin Tinubu suna fitowa don mayar da martani ga yan adawa.
"Su 'yan tsiraru ne, kuma fadar Shugaban kasa ba su tsorata da su ba, amma mu ma, kuma ina nufin shugabanninmu na siyasa, ministoci da masu an ba mu umarni mu fita filin kamfe don kalubalantar masu suka daga cikin manyan Arewa."

Wata majiya mai tushe daga fadar Shugaban kasa ta ce banda umarnin da aka ba masu rike da mukaman siyasa na Arewa, an bukaci su sake tallata Shugaban kasa a yankin.

Kara karanta wannan

Sabon limamin Abuja ya yi nasiha mai zafi ga malamai masu jifan juna ta intanet

"Batun ya fi kawai burin Shugaban kasa na 2027, da dama daga cikin ‘yan siyasa daga Arewa da ke cikin gwamnati sun fahimci abin da rashin goyon bayan Tinubu a 2027 zai haifar."
"Yayin da wasu jiga-jigan siyasa daga Arewa, ciki har da Sanata Wammako da Nasir El-Rufai, ke kokarin hana Tinubu tsayawa takara a 2027, Kashim Shettima, da wasu ministoci suna kokarin ganin shugabancin kasa ya koma Arewa maso Gabas."

Cewar majiyar

Fadar shugaban kasa ta yi magana

A nata bangaren, fadar Shugaban kasa ta ce ba ta tilasta wa ministocin Arewa su kare Tinubu ba, domin suna yin aikinsu ne kawai.

Mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin labarai da dabaru, Mista Bayo Onanuga, ya ce:

"Wadannan ministoci suna yin aikinsu, babu wanda ya umarce su su mayar da martani.
"Suna aikinsu ne kawai, Idan ka ga mutane da dama suna fadin abin da suka ga dama, dole wani ya mayar da martani ya fadi gaskiya.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga sama da 100 suka taru wajen sace Janar Tsiga a Katsina

Matawalle ya kalubalanci Amaechi kan kalamansa

Kun ji cewa Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya soki kalaman tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, inda ya zarge shi da tunzura jama'a.

Ministan tsaro ya yi gargadi ga Rotimi Amaechi da duk wani da zai yi kokarin tunzura jama’a ko tayar da tarzoma a tsakanin 'yan kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.