Tsohon Gwamnan APC Ya Tona Sirrin 'Sabanin' da ke tsakanin 'Yan Siyasa

Tsohon Gwamnan APC Ya Tona Sirrin 'Sabanin' da ke tsakanin 'Yan Siyasa

  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya ce fadace-fadace tsakanin ‘yan siyasa ba ya jawo wata kiyayya mai zafi kamar yadda a kan yayata
  • Fayemi ya tabbatar da cewa a lokuta da yawa, masu amfani da shafukan sada zumunta ne su ke kumura sabani a tsakanin 'yan siyasa fiye da kima
  • Ya jaddada cewa duk sabanin siyasa da ake gani a tsakanin 'yan siyasa, amma su na da kyakkyawar alaka da junansa a duk inda su ke a rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ekiti -Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, ya musanta zargin da ke cewa rikici tsakanin ‘yan siyasa na haifar da kiyayya a tsakaninsu.

Ya bayyana hakan ne a yayin bikin cikar sa shekaru 60 da aka gudanar a Cocin Katolika na St. Martin’s da ke Isan Ekiti a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Buhari ya ajiye girma ya yi jinjina ga wanda ya taimaka masa sosai a 2015

Tsohon gwamna
Tsohon gwamna ya ce babu kiyayya a tsakanin 'yan siyasa Hoto: Kayode Fayemi
Asali: Facebook

Vanguard ta ruwaito cewa Fayemi ya yi watsi da ra’ayin cewa akwai kiyayyar gaske a siyasa, musamman wacce kafofin sada zumunta ke kara rurawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa wadannan rikice-rikicen da ake gani a siyasa, hanya ce kawai ta nishadantar da ‘yan Najeriya.

'‘Yan siyasa ba makiyan juna ba ne' – Fayemi

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya ce duk da bambancin jam’iyya da siyasa, ‘yan siyasa, musamman na Jihar Ekiti, ba makiyan juna ba ne.

A cewarsa:

"Duk abubuwan da kuke karantawa a kafafen sada zumunta na nishadantar da ku ne kawai.
"Wasu za su yi mamakin ganin Gwamna Segun Oni a nan. A ranar haihuwarsa, na kwashe duk ranar tare da shi. Haka ma Gwamna Ayodele Fayose da ba zai yi kasa a guiwa ba idan yana nan."

Tsohon gwamnan ya bayyana farin cikinsa yayin da ya ke kallon nasarorin da ya shafe a siyasa da kuma cikar sa shekaru 60 a duniya.

Kara karanta wannan

"Shirin gwamnati ya gaza, " Tsohon gwamnan APC ya fito da matsalolin mulkin Tinubu

Fayemi ya ce:

"Ina da dalilai da dama da za su sa in gode wa Allah a wannan lokaci.
"Ina kuma gode wa gwamnanmu da na ke alfahari da shi. Hakan da ya faru na iya mai kima. Duk da wahalhalun da ake fuskanta a duniyar siyasa, muna da kyakkyawar alaka wacce ta dogara ne kan soyayya da mutunta juna."

Fayemi ya shawarci gwamnatin tarayya

A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon gwamna, Kayode Fayemi ya bayyana cewa shirye-shiryen gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na farfado da tattalin arzikin kasa ba su haifar da sakamakon da ake bukata ba.

Ya shawarci gwamnati ta sake duba manufofinta ta yadda ba za ta wahalar da jama'a sosai ba, inda ya ce a halin da ake ciki, an tsare-tsaren tattalin arzikin sun jefa jama'a a cikin matsin rayuwa matuka.

Dr. Fayemi ya kara da cewa ya kamata shugabannin kasar nan su gaggauta neman gafarar 'yan Najeriya, ganin yadda su ka jefa rayuwarsu a cikin wahala, sabanin alkawuran da su ka yi gabanin zabarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.