'Shi Zai Iya Gyara Najeriya': Dan PDP Ya Roki Kwankwaso, Obi Su Hade da Atiku Abubakar
- Surajo Yunusa Caps ya nemi tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar da ya daura damarar yin takara a zaben 2027
- Dan jami'yyarr na PDP ya ce Atiku zai ba matasa dama idan ya ci zabe, kuma zai cire kasar daga matsalolin tattalin arziki da take ciki
- Surajo ya kawo dabarar kayar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu a zabe mai zuwa, inda ya nemi hadin kan 'yan jam'iyyun adawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Wani matashi dan jam'iyyar PDP, Surajo Yunusa Caps ya nemi Peter Obi, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da su hade da Wazirin Adamawa gabanin 2027.
Surajo Caps ya ce yana da tabbacin cewa Atiku Abubakar zai iya lallasa shugaba Bola Tinubu a zaben 2027, musamman idan ya samu goyon bayan 'yan adawa.

Asali: Facebook
A wata tattaunawa ta musamman da Legit Hausa a ranar Alhamis, 6 ga Fabrairun 2025, Suraj Caps ya ce ya taka takanas har gidan Atiku Abubakar don ba shi shawarwari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Atiku zai ba matasa dama" - Surajo Caps
Game da ziyarar da ya kai wa Atiku, matashin dan siyasar ya ce:
"Ita ziyara ta shafi yanayin da al'umma take ciki, da kuma yadda al'ummar kasa ke bukatar ta samu yanayi na sauki na rayuwa.
"A yadda muka yi la'akari da yadda abubuwa ke tafiya. Shi ne muka yi la'akari da cewa Atiku ne ya fi cancanta a karfafa, da ba shi shawarwari kan zaben 2027 mai zuwa."
Suraj Caps ya ce Atiku Abubakar ya ba shi tabbaci na cewar zai ba matasa karfi a cikin al'amuransa, tun daga yakin neman zabe har zuwa idan Allah ya sa ya ci zabe.
"Shi Wazirin Adamawa yana da buri na ganin cewa matasa sun shigo cikin harkar siyasa don ganin an buga da su tare da nemo hanyar fitar da kasar daga halin da take ciki."

Kara karanta wannan
Matasan Arewa sun fadi sunayen 'yan siyasa 3 da ke shirin ruguza gwamnatin Tinubu
- Surajo Caps.
Ya kamata Atiku ya hakura da takara a 2027?
A baya bayan nan, Legit Hausa ta rahoto cewa jigon PDP, George Akume ya roki Atiku Abubakar ya hakura da neman takarar shugaban kasa haka nan.
Akume, wanda tsohon mataimakin shugaban PDP na kasa ne, ya ce lokaci ya yi da Atiku zai hakura da yin takara, bayan shekaru 31 yana neman mulki.
Dangane da ire-iren wadannan kiraye-kirayen, Surajo Caps ya yi martani da cewa:
"Shi wannan zance da ake yi 'yanci ne, kowane dan kasa na da 'yancin fadin haka. Amma mu siyasa muke yi, kuma siyasa tana bukatar lissafi.
"Idan ka kalli gwamnatin shi Asiwaju da take ci yanzu, sannan ka dauko sauran 'yan takara, ka ce su sauya gwamnatin mai ci, to gaskiyar zance in ba Atiku Abubakar ba, ban yi tsammanin akwai wanda zai iya wannan ba."
Dan jam'iyyar na PDP ya yi ikirarin cewa akwai shugabannin kasashe na duniya da sun girmi Atiku Abubakar, kuma hakan bai hana a zabe su ba.

Kara karanta wannan
"Me suke shiryawa?": Ziyarar da Atiku Abubakar ya kai wa Sanata Binani ta bar baya da ƙura
"Yanzu idan ka kalli Donald Trump a Amurka, tsoho ne kuma ya girmi Atiku. Mu bukatarmu ba yaro ko tsoho ba, damuwarmu wanda zai kawo mana mafita a yanayin da muke ciki."
'Abin da na fadawa Atiku' - Surajo Caps
Matashin dan siyasar ya ce, akwai maganar da ya fadawa Atiku a yayin ganawarsu, kan yadda gwamnatin ta ke gudanar da mulkinta.
Surajo Caps ya ce:
"Na ce masa ya godewa Allah da ya yi masa tsawon rai bai dauki rayuwarsa ba, ya ga wasu abubuwa. Ya ce mani 'menene Surajo?
"Na ce masa duk sharrin da aka yi maka, duk makircin da aka yi maka, aka ce in ka zama shugaban kasar Najeriya aka ce za ka yi wa Najeriya, sai da wadannan mutanen na APC suka yi irinsa, suka yi wanda ya wuce irinsa.
"Idan ka duba, kamar yadda suka ce idan ya zo zai mayar da NNPC hannun 'yan kasuwa, to shi tsarin da Atiku ya yi ba irinsa ne su suka yi ba.
"Su a lokacin suna masa adawa matsayin zai sayarwa abokansa ne, to su kuma da suka zo sai harkar ta zamo ta iyalansu, sannan sai man ma ya gagari talaka."
Matashin ya ce zuwan gwamnatin APC ya jawo kamfanoni da dama sun rufe tare da barin Najeriya maimakon a samu karuwarsu.
An nemi 'yan adawa su hada kai da Atiku
Surajo Caps ya nemi 'yan takarar Adawa, irinsu Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Peter Obi da su sanya kasarsu a gaba ba wai burin kashin kansu ba.
"Duk masu son neman takarar shugaban kasa, da masu son kalubalantar wannan gwamnatin, su kalli kasar, su kalli karfin APC, su kalli halin da talakawa suke ciki.
"Su tausayawa talakawa fiye da bukatar kansu, su hada hannu karfi da karfe, su taimaki Atiku su mara masa baya, to in sun yi haka, tarihi ba zai manta da su ba."
"Sannan kuma mutanen Arewa, mu kara wayewa, ka da mu yi zaben taliya. Kowa ya yarda cewa zai iya ba da gudunmawa domin kawo sauyi a kasar nan."
- Surajo Caps.
Atiku ya magantu kan kalaman Akume
A wani labarin, mun ruwaito cewa Atiku Abubakar ya yi martani ga George Akume kan cewa masu neman takarar shugaban kasa daga Arewa su jira zuwa 2031.
Atiku ya tunatar da Akume cewa yankin Kudu sun fi Arewa dadewa a kan mulki, kuma 'yan Najeriya ne ke da ikon zabar wanda suke so ya zama shugabansu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng