NNPP: "Har Yanzu Kwankwaso, Abba Halastattun 'Yan Jam'iyya ne"
- Shugaban jam'iyyar adawa ta NNPP ya yi watsi da korar da tsagin Agbo Major ya yi wa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf
- Sakataren yada labaran NNPP na kasa, Ladipo Johnson ya bayyana cewa daya tsagin ba shi da ikon yin magana a madadin jam'iyyar a hukumance
- Ya kara da cewa dokar kasa da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) sun amince da Ahmed Ajuji da mukarrabansa a matsayin shugabannin NNPP
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - NNPP ta sake jaddada cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, har yanzu 'yan jam’iyyar ne.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Ladipo Johnson, ne ya bayyana hakan yayin taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a ranar Litinin a babban birnin tarayya, Abuja.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa Mista Johnson ya jaddada cewa shugabancin jam’iyyar da ke karkashin jagorancin Ajuji Ahmed—wanda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta amince da shi—shi ne kadai ke da ikon yin magana da sunan jam’iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ajuji ne shugaban jam'iyyar NNPP" – Johnson
Ladipo Johnson ya bayyana cewa Shugaban NNPP na kasa, Ajuji Ahmed, shi ne wanda doka ta amince da shi a matsayin wanda ke jagorantar jam’iyyar.
A cikin sanarwar da ya fitar, Mista Johnson ya ce:
“INEC, idan za a bi doka, ta amince da NNPP a karkashin jagorancin Dokta Ajuji Ahmed a matsayin shugaban jam’iyya da kuma ni, Ladipo Johnson, a matsayin sakataren yada labarai.
“Wannan shi ne abin da doka ta tabbatar a yau. Wannan bangaren jam’iyyar bai kori ko dakatar da Abba Yusuf ko Rabiu Kwankwaso ba.”
Bayanin jam'iyyar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun rikici a shugabancin jam’iyyar, inda ake ta dakatarwa da korar juna tsakanin shugabanninta.
Yadda rikicin jam'iyyar NNPP ya samo asali
Rikicin ya samo asali ne daga wata takaddama ta mulki da ta hada da daya daga cikin masu kafa jam’iyyar, Dokta Boniface Aniebonam.
Johnson ya bayyana cewa kokarin da Aniebonam ya yi na yin watsi da hukuncin Kwamitin Majalisar Koli (NEC) da Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) ya kai ga dakatar da shi daga jam’iyyar.
Ya ce:
“Dokta Boniface Aniebonam yana daga cikin wadanda suka kafa NNPP. Sanata Kwankwaso, Buba Galadima, ni da wasu mun shiga jam’iyyar a shekarar 2022.
“Shekara daya kafin zaben 2023, matsaloli suka fara. Daga nan ne Aniebonam ya fara ikirarin cewa shi ne ke da iko a kan NEC da NWC na jam’iyyar.
“Mun bijire wa wannan lamari, wanda hakan ya kai ga dakatar da shi. Har Kwankwaso ma bai san cewa za a dakatar da shi ba.”
'NNPP' ta kori Kwankwaso daga jam'iyya
A baya, kun ji cewa tsagin Agbo Major na NNPP ya tabbatar da cewa an kori Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Kwankwasiyya daga jam’iyyar, yayin da rikicin shugabanci ya yi kamari.
A yanzu, rikicin NNPP na ci gaba da daukar sabon salo, inda kowane bangare ke yin ikirarin cewa shi ne halastaccen dan jam'iyya, yayin da tsagin Kwankwaso ke cewa shi doka ta sani a matsayin shugaban jam'iyya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng