Tasirin Ganawar Kwankwaso da Aregbesola a kan Siyasar Tinubu a 2027

Tasirin Ganawar Kwankwaso da Aregbesola a kan Siyasar Tinubu a 2027

  • Rahotanni sun nuna Rabiu Kwankwaso yana kokarin jawo tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, domin samun goyon baya a Kudu
  • A ranar Asabar da ta gabata, Sanata Kwankwaso ya gana da Aregbesola a gidansa da ke Legas a wani zama da suka yi da ya hankalin al'umma
  • Wani jigo a Kwankwasiya ya bayyana cewa Aregbesola zai iya zama wata hanya ga Kwankwaso domin kutsa kai cikin siyasar Kudu maso Yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Ganawar sirri da aka yi tsakanin jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya janyo ce-ce-ku-ce.

Ana ganin cewa ganawar na daga cikin dabarun Kwankwaso na neman goyon baya a yankin Kudu maso Yamma yayin da ake shirin tunkarar zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya gana da tsohon gwamnan APC, an yi hasashen shirin tumbuke Tinubu

Kwankwaso
Tattaunawar kan 2027 da aka yi tsakanin Kwankwaso da Aregbesola a kan 2027. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso|Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa akwai yiwuwar wannan tattaunawa ta zama matakin haɗin gwiwa tsakanin su domin fafutukar siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar shigan Aregbesola cikin Kwankwasiyya

Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya ya bayyana cewa Kwankwaso yana neman yin amfani da tasirin Aregbesola domin samun goyon baya a Kudu maso Yamma.

Jigon ya bayyana cewa:

"Kwankwaso yana da burin faɗaɗa tasirinsa fiye da Arewa, amma yana fuskantar matsala saboda yawan magoya bayan Tinubu a Kudu maso Yamma.
"Aregbesola na iya zama wata dama gare shi musamman a Legas da Osun, inda yake da tasiri sosai,"

Kwankwaso na fuskantar ƙalubale wajen samun tasiri a yankin, amma fitowar Aregbesola daga jam’iyyar APC na iya zama wata dama gareshi domin samun tagomashi a yankin.

A kwanakin baya, ƙungiyar siyasa ta Aregbesola ta fice daga APC a jihar Osun, lamarin da ya ƙara jayo ce-ce-ku-ce game da makomarsa a siyasa.

Kara karanta wannan

'Yar hassada ce': Musa Kwankwaso ya soki Naja'atu, ya jero manyan da ta zaga

NNPP: Kwankwaso ya gana da Aregbesola

Kakakin jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya tabbatar da cewa ganawar da aka yi tsakanin Kwankwaso da Aregbesola na cikin shirin hadin kai tsakanin Arewa da Kudu maso Yamma.

Ya kuma bayyana cewa babu wanda zai tilasta wa Aregbesola yin biyayya ga wata tafiya ta siyasa, domin ya kasance ɗan siyasa mai dogon tarihi da ƙarfi a matakin ƙasa.

"Idan har ya fice daga APC, yana da cikakken ‘yanci a siyasa. Kafin yanzu, ya taɓa nuna rashin goyon baya ga Tinubu a 2023, amma hakan bai hana shi cigaba da tasiri a siyasa ba,"

- Ladipo Johnson

Tasirin hadakar Kwankwaso da Aregbesola

A cewar Johnson, Kwankwaso da Aregbesola sun shahara wajen yin siyasar tuntuɓar jama’a kai tsaye, kuma hakan zai yi tasiri a zabukan 2027.

"A halin yanzu, ban ga alamar Aregbesola na shirin tsayawa takara ba. Amma zai iya zama babban abokin haɗin gwiwa ga Kwankwaso a Kudu maso Yamma,"

Kara karanta wannan

'Diyar Ganduje ta samu babban mukamin gwamnati, majalisa ta aika sunaye ga Tinubu

- Ladipo Johnson

Ya ƙara da cewa idan har Kwankwaso ko Aregbesola ba su tsaya takara ba, za su iya yin tasiri matuƙa a siyasar Najeriya.

NNPP ta kori Sanata Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban tsagin jam'iyyar NNPP ya jaddada korar Sanata Rabi'u Kwankwaso da Buba Galadima.

Haka zalika, tsagin jam'iyyar ya bukaci dukkan magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya da su fita daga tafiyar ba tare da bata lokaci ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng