'Yadda Gwamnonin PDP Ke Shirin Kafa Sabuwar Jam'iyya domin Komawa Cikinta'

'Yadda Gwamnonin PDP Ke Shirin Kafa Sabuwar Jam'iyya domin Komawa Cikinta'

  • Sanata Sam Anyanwu ya zargi gwamnonin PDP da kwamitin amintattu, BoT da kokarin tsige shi saboda dangantakarsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike
  • Ya ce gwamnonin PDP na shirin kafa sabuwar jam’iyya, kuma kiran da ake yi na nada Sunday Udeh-Okoye a matsayin Sakatare wata makarkashiya ce
  • Anyanwu ya kara da cewa gwamnonin suna haddasa rikici ne don samun hujjar sauya sheka zuwa sabbin jam’iyyun da suke shirin kafawa nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Sanata Sam Anyanwu, wanda ake takaddama kan kujerarsa a matsayin Sakatare Janar na jam’iyyar PDP, ya yi tone-tone.

Sanata Anyanwu ya zargi gwamnonin PDP da kwamitin amintattu (BoT) da kokarin tsige shi saboda kusancinsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike.

An zargin gwamnonin PDP da shirin kafa sabuwar jam'iyya
Sanata Sam Anyanwu ya zargi PDP da shirin kirkirar wata jam'iyya domin su sauya sheka. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Twitter

An zargi gwamnonin PDP da makarkashiya

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya gana da tsohon gwamnan APC, an yi hasashen shirin tumbuke Tinubu

A wata hira da yayi da jaridar Tribune, Anyanwu ya bayyana cewa gwamnonin PDP na shirin kafa sabuwar jam’iyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma, ya ce kiran da ake yi na nada Sunday Udeh-Okoye a matsayin Sakatare wani bangare ne na "yakin neman iko" da gwamnonin ke jagoranta.

Jam’iyyar PDP na fama da rikicin cikin gida, wanda ya samo asali daga bangaren da ke tare da Wike da kuma wadanda ke adawa da tasirinsa a cikin jam’iyyar.

Anyanwu, wanda aka san yana tare da Wike, ana kallonsa a matsayin daya daga cikin amintattun tsohon gwamnan Jihar Ribas, wanda ya mara masa baya a zaben gwamnan Imo.

Ya jaddada cewa ana kokarin ganin bayansa ne kawai saboda dangantakarsa da Wike.

“Gaskiyar magana ita ce suna yakina ne a boye, Sun san cewa ina tare da Wike, shi ke nan, babu wata matsala tsakanina da su.
“Kungiyar gwamnonin PDP wata kungiya ce ta son rai, kowane gwamna na iya shiga ko kin shiga."

Kara karanta wannan

'Diyar Ganduje ta samu babban mukamin gwamnati, majalisa ta aika sunaye ga Tinubu

- Sam Anyanwu

Jigon PDP ya bugi kirji kan kujerarsa

Anyanwu ya yi watsi da sahihancin matakin da gwamnonin da BoT suka dauka, yana mai cewa ba su da ikon yin hakan a kundin tsarin jam’iyyar.

Ya jaddada cewa ya rike matsayinsa na sakatare tun kafin yawancin gwamnonin yanzu su hau kan mulki.

Anyanwu ya zargi wasu gwamnonin PDP da haddasa rikici a cikin jam’iyyar don su sami dalilin sauya sheka zuwa sabbin jam’iyyun da suke shirin kafawa.

“Babu wata matsala a cikin jam’iyyar, suna haddasa tashin hankali ne kawai don su samu damar komawa jam’iyyun da suke shirin kafawa."

- Cewar Sam Anyanwu

Kwamitin amintattun PDP ya yi ganawar gaggawa

Kun ji cewa bayan rikicin da ya faru har aka ba hammata iska a makon jiya, majalisar amintattun PDP watau BoT ta kira taron gaggawa a Abuja.

An ruwaito cewa taron ya gudana ne a ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairu, 2025 a wani otal da ke birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.