Yan fashi
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya shirya yakar matsalolin kwacen waya da kuma ta'ammali da miyagun kwayoyi da ya yi katutu a fadin jihar baki daya.
Wasu 'yan bindiga dauke da manyan makamai da suka hada da AK-47 sun farmaki sansanin jami'an tsaro a jihar Katsina. Sun kuma tafka barna a kauyen Nahuta.
Mayakan ISWAP sun yanke danyen hukunci kan wasu masunta guda biyu bayan da suka kama su kan zargin sun yi masu satar kifi a wani kauyen jihar Borno.
Rundunar 'yan sanda ta sallami wasu jami'anta guda biyu tare da shirin gurfanar da su gaban kotu. An kama su da laifin aikata fashi da makami tare da 'yan bijilante.
Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun kashe mutum hudu da suka je siyayya a babban kantin siyar da kaya na Wisfom da ke a Nasarawa.
Sheikh Ahmad Gumi ya ce kashe biliyoyin naira wajen siyo makaman da aka yi su a Yakin Duniya II don yaki da 'yan ta'adda tsohon yayi ne. Ya nemi a tattauna da su.
Gwamnatin jihar Sokoto ta kaddamar da sabuwar rundunar tsaron al'ummar jihar. Gwamna Aliyu ya ce rundunar tsaron al'ummar ba kishiyar 'yan sanda ba ce.
Rundunar 'yan sanda a jihar Adamawa ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun farmaki garin Kwapre da ke karamar hukumar Hong a jihar.
Rundunar 'yan sanda a jihar Edo ta bankado wani mummunan labari inda 'yan fashi suka yi wa wata gawa fashi a cikin mota a birnin Benin City da ke jihar.
Yan fashi
Samu kari