Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Tare Motar Makaranta, Sun Sace Dalibai da Dama

Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Tare Motar Makaranta, Sun Sace Dalibai da Dama

  • A wani yanayi maras dadi, wasu 'yan bindiga sun tare motar da ake daukar yara zuwa makaranta, sun yi awon gaba da dalibai masu yawa
  • Har zuwa yanzu dai ba a samu wani cikakken bayani kan yawan daliban, ko makarantar da daliban suke ba, amma lamarin ya faru a jihar Ekiti
  • Sace daliban na zuwa kwanaki kadan bayan da wasu 'yan bindiga suka kashe wasu sarakunan gargajiya guda biyu a jihar ta Ekiti

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ekiti - Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi awon gaba da wasu yara ‘yan makaranta da ba a tantance adadinsu ba a karamar hukumar Emure da ke jihar Ekiti a yammacin jiya.

Kara karanta wannan

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fi ko ina yawan masu garkuwa da mutane, in ji Seun Kuti

Duk da cewa har yanzu ba a samu cikakken bayani kan harin ba, kuma ba a bayyana sunan makarantar da aka sace wa daliban ba.

Yan bindiga sun tare motar makaranta, sun sace dalibai da dama.
Ekiti: Yan bindiga sun tare motar makaranta, sun sace dalibai da dama. Hoto: @biodunaoyebanji
Asali: Twitter

Yan bindiga sun kashe sarakunan gargajiya biyu a Ekiti

An tattaro cewa ana tsaka da tafiya da daliban ne a cikin motar makarantarsu, a kan iyakar Eporo-Ekiti lokacin da lamarin ya faru, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har yanzu dai ba a san adadin daliban da ke cikin hannun masu garkuwa da mutanen ba kuma har yanzu ‘yan sanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.

Lamarin ya biyo bayan kashe sarakunan gargajiya biyu a jihar; Onimojo na Imojo Ekiti, Oba Olatunde Samuel Olusola da kuma Elesun na Esun Ekiti, Oba David Babatunde Ogunsola.

Gwamna Oyebanji ya sha alwashin kama 'yan bindigar

Arise News ta ce wasu ‘yan bindiga ne suka yi musu kwanton bauna a lokacin da suke dawowa daga wani taro. Amma wani basaraken, Alara na Ara –Ekiti, Oba Adebayo Fatoba ya sha da kyar.

Kara karanta wannan

Kudin Fansa: Masu garkuwa suna barazanar hallaka mutanen Abuja 11 da aka sace

Gwamnan jihar, Biodun Oyebanji, wanda ya yi Allah wadai da wannan danyen aiki, ya umarci jami’an tsaro a jihar da su kamo wadanda suka kashe sarakunan biyu, rahoton Daily Post.

Biodun Oyebanji, ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gano bakin zaren lamarin.

Daliba ta sha gubar bera saboda saurayinta ya rabu da ita

A wani labarin, wata dalibar kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da me Mubi, jihar Adama, mai suna Jamima Shetima Balami ta dauki ranta da kanta saboda haushin rabuwa da saurayinta.

An ruwaito cewa Jamima ta sha gubar bera, bayan da saurayin nata da ake zargin malamin jami'a ne ya nemi su kawo karshen soyayyar da ke a tsakanin su,

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel