Yan Bindiga Sun Kai Hari a Wani Babban Kanti a Jihar Nasarawa, Sun Kashe Mutum 4

Yan Bindiga Sun Kai Hari a Wani Babban Kanti a Jihar Nasarawa, Sun Kashe Mutum 4

  • Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun kashe mutum hudu a wani hari da suka kai babban kantin Wisfom a Nasarawa
  • Rahotanni sun ce 'yan fashin sun shiga kantin ne misalin karfe 8:45 na daren ranar Talata, inda suka kashe namiji uku da mace daya
  • Tuni kwamishinan 'yan sandan jihar Nasarawa Umar Nadada ya ba da umurnin gudanar da binciken gaggawa don kama masu laifin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Nasarawa - Akalla mutum hudu ne aka kashe a ranar Talata bayan wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a wani babban kanti a karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kantin Wisfom da misalin karfe 8:45 na dare inda suka kashe maza uku da wata mace daya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake Afka wa kauyen Neja, sun sace mata da miji da karamin yaro

Yan bindiga sun kashe mutum hudu a Nasarawa
Yan bindigar sun kai farmaki kantin Wisfom a jihar Nasarawa inda suka kashe maza uku da wata mace daya. Hoto: @NGPolice
Asali: Twitter

Mazauna yankin sun ce lamarin ya fara damunsu tun da yanzu ba sa samun zaman lafiya a jihar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar 'yan sanda za ta fara bincike kan farmakin

Daya daga cikin mazauna garin, Adamu Jacob ya bada misali da sace shugaban Akwanga, Isa Andaha da wasu mutane uku a ranar Litinin, 25 ga watan Disamba, 2023.

Sai kuma batu kan sace wani malami a Kokona da wasu dalibai a jami'ar tarayya ta Lafia da kuma jami'ar jihar Nasarawa dake Keffi.

The Guardian ta ruwaito cewa kakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, DSP Ranham Nansel ya ce ‘yan bindigar sun mamaye kantin da daddare.

A wani rahoton jaridar The Punch, kwamishinan 'yan sandan jihar Umar Nadada ya ba da umurnin gaggauta yin bincike don gano wadanda suka aikata danyin aikin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun harbe dan banga, sun yi garkuwa da mutum 3 a babban birnin tarayya Abuja

Yan bindiga sun kashe dan banga, sun sace mutum uku a Abuja

A wani labarin kuma, wasu ‘yan bindiga sun sace mutum uku a kauyen Barangoni da ke gundumar Bwari da ke birnin tarayya Abuja.

A yayin harin ne kuma aka ruwaito cewa 'yan bindigar sun harbe wani dan banga mai suna Samson, kamar yadda wani mazaunin Barangoni mai suna Joshua Madaki ya shaida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel