An kama wani matashi da ya kware wurin satar kayan coci, za a gurfanar da shi

An kama wani matashi da ya kware wurin satar kayan coci, za a gurfanar da shi

  • Jami'an tsaro na kungiyar So-Safe ta kama wani matashi da ya juma yana yin sata a wuraren bauta a yankin Ado-Odo/Ota, jihar Ogun
  • Jami'an sun kama barawon ne a ranar Lahadin da ta gabata, bayan da ya saci wasu kayayyaki a wata coci yana kokarin tserewa da su
  • Matashin ya amsa laifin sa, kuma ya lissafa coci-coci da ya yi wa sata da suka hada da Redeemed Christian Church of God, Baba Ode da sauran su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kungiyar tsaro ta So-Safe a jihar Ogun ta kama wani barawo mai suna Biola Adebesin, wanda ta yi zargin ya kware wajen yin sata a coci-coci a garin Baba Ode da Iju a yankin Ado-Odo/Ota.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da gobara ta cinye tsohuwa mai shekaru 80 a jihar Benue

Ana zargin Adebesin da yin sata a cocin Redeemed Christian Church of God, Onibuku, Cherubim and Seraphim, Baba Ode da Stronghold Ministry".

An kama wani matashi da ya ‘kware’ wurin sata a coci-coci
An kama wani matashi da ya ‘kware’ wurin sata a coci-coci a jihar Ogun. Hoto: Soji Ganzallo
Asali: Facebook

Jerin irin kayayyakin da ya ke sata

New Telegraph ta ruwaito kayayyakin da aka kwato daga gare shi sun hada da na'urar buga kida kirar Yamaha guda biyu, na'urar hada sauti guda daya, na'urar dikoda,.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran kayan sun hada da wasu kayan masarufi, wayar Tecno guda daya da kananan wayoyin Bontel.

Hakan ya fito ne a ranar Lahadin da ta gabata daga ofishin kwamandan rundunar na jihar, Soji Ganzallo ta ofishin Daraktan yada labarai na rundunar, Moruf Yusuf, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Matashin ya amsa laifin yin sata a wuraren bauta

Ganzallo, a cikin sanarwar, ya ruwaito cewa:

"A ranar 18 ga watan Junairu, 2024, jami’an hukumar dake sintiri na yau da kullum sun yi artabu da wanda ake zargin dauke da kayan sata a unguwar Baba Ode.

Kara karanta wannan

"A nemo mun ita: Bidiyon wata yar makaranta tana Sallah a kan hanya ya dauka hankalin jama'a

"Wanda ake zargin ya amsa laifin yin sata a cocin Redeem Christian Church of God, Onibuku, Cherubim and Seraphim, Baba Ode da Stronghold Ministry."

Ganzallo ya bayyana cewa, wanda ake zargin, Adebesin, an mika shi zuwa hedikwatar ‘yan sanda ta Onipaanu domin ci gaba da bincike kuma ana iya gurfanar da shi gaban kuliya.

Yan bindiga sun kashe shugaban makarantar sakandare a Kaduna

A wani labarin, wasu gungun 'yan bindiga sun kashe wani Idris Abu Sufyan, wanda shugaban makarantar sakandare ne a karamar hukumar Chukun, da ke jihar Kaduna.

An ruwaito cewa yan bindigar sun kashe Abu Sufyan saboda ya ki yarda su tafi da shi, kuma sun tafi da wasu mata biyu a yayin farmakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel