Inna Lillahi: An Sake Kai Hari Wata Jihar Arewa, an Kashe Mutum Biyu Tare da Yin Mummunar Barna

Inna Lillahi: An Sake Kai Hari Wata Jihar Arewa, an Kashe Mutum Biyu Tare da Yin Mummunar Barna

  • Wasu 'yan bindiga da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai farmaki wani kauyen karamar hukumar Hong da ke jihar Adamawa
  • A yayin farmakin, sun kashe mutum biyu tare da jikkata wasu, sannan sun yi awon gaba da kayan abinci inda suka shige cikin dajin Sambisa
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da lamarin tare da bayyana cewa ta tura jami'ai don farautar wadanda ake zargin sun aikata laifin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Adamawa - Rundunar 'yan sanda a jihar Adamawa ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun farmaki garin Kwapre da ke karamar hukumar Hong a jihar.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, 'yan bindigar sun kai sabon hari a ranar Litinin (ana tsaka da bikin kirsimeti), inda aka yi asarar rayuka.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ƴan bindiga sun kai ƙazamin hari ana shirin taron addini a arewa, sun kashe sama da 15

Yan bindiga sun kashe mutum biyu a Adamawa
Rundunar 'yan sanda a Adamawa ta ce wasu 'yan bindiga sun farmaki garin Kwapre tare da kashe mutum biyu a jihar. Hoto: @NGPolice
Asali: Facebook

'Yan sanda sun tabbatar da kai farmaki garin garin Kwapre

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar SP Suleiman Nguroje ya bayyana hakan ga manema labaraia a Yola a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Labarin harin da jaridar Daily Trust ta fitar na zuwa ne jim kadan bayan da sanarwa ta fita na yadda 'yan bindiga suka farmaki wani gari a jihar Plateau, daruruwan mutane sun mutu.

Kungiyar gwamnonin Arewa ta yi Allah wadai da wannan harin kisan gillar da aka kai Plateau tare da ba da umurnin kamo wadanda suka aikata danyen aikin.

Hakimin Gugwaba ya magantu kan kisan mutum biyu

A kan harin jihar Adamawa kuwa, SP Nguroje ya ce rundunar na ci gaba da bincike bisa umurnin kwamishinan 'yan sandan jihar Babtola Afolabi.

Jaridar Leadership ta ruwaito hakimin Dugwaba, Mr Simon Buba a zantawarsa da manema labarai ya tabbatar da kisan mutum biyu yayin harin 'yan bindigar.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da shirin Kirsimeti, 'yan bindiga sun sheke gomman mutane a jihar Filato

Ya kara da cewa suna zargin cewa 'yan bindigar mayakan Boko Haram ne wadanda suka mamaye garin akan babuwa tare da yin awon gaba da kayan abinci tare da shiga dajin Sambisa.

Fursunoni uku sun tsere daga gidan gyaran hali na jihar Ogun

Wani sabon labari na nuni da cewa wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan gyara hali na Ijebu Ode da ke karamar hukumar Ijebu Ode, jihar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewa fursunonin sun tsallake katanga tare da arcewa a safiyar ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel