Rashin Tsaro: Shehu Sani Ya Fadi Jerin Matsaloli 7 da Arewacin Najeriya Ke Fama da Su

Rashin Tsaro: Shehu Sani Ya Fadi Jerin Matsaloli 7 da Arewacin Najeriya Ke Fama da Su

  • Sanata Shehu Sani ya zayyana yadda jihohin Arewa ke fama da hare-haren 'yan ta'adda, fadan kabilanci da ma na addini wanda ya gusar da zaman lafiya a shiyyar
  • Shehu Sani ya ce Arewa na fuskantar wasu nau'ikatan rikice-rikice guda bakwai, tare da alakanta kowacce jiha da matsalar da take fama da ita
  • Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a 26 ga watan Janairu, Sanata Sani ya ce 'yan ta'adda, 'yan fashin daji sun fi ta'adi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Shehu Sani, ya ce Arewacin Najeriya na fama da wasu matsaloli guda bakwai da suka haifar da rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: Kwanaki 3 da Suka Wuce Tinubu Ya Saki Kudin Manyan Ayyuka 3 Inji Minista

Bayanin sanatan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun hare-haren 'yan bindiga, ƙabilanci da addini a wasu sassa na Arewacin ƙasar.

Jerin matsaloli 7 da Arewacin Najeriya ke fama da su
Rashin tsaro: Jerin matsaloli 7 da Arewacin Najeriya ke fama da su, in ji Shehu Sani. Hoto: @ShehuSani
Asali: Facebook

Ga jerin matsalolin da jihohin Arewa ke fuskanta kamar yadda Sanata Sani ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, 26 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. 'Yan fashin daji

Shehu Sani ya ce hare-haren 'yan bindiga ya fi yawaita a jihohin Arewa maso Yammacin kasar da suka hada da Zamfara, Katsina, Sokoto, Kebbi da Niger.

2. 'Yan ta'adda

A cewar Sanata Sani, jihohin Yobe da Borno sun fi fuskantar hare-haren 'yan ta'adda, wadanda manufarsu ita ce kashe mutane ba gaira babu dalili da kona muhallansu.

3. Yan fashin daji da 'yan ta'adda

A jihohin Kaduna da Niger kuwa, tsohon sanatan ya ce ana samun hare-haren 'yan fashi da 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ki karbar cin hancin naira miliyan 1, sun kama dan bindiga a otal din Kaduna

Yayin da 'yan fashin daji ke yin garkuwa da mutane don kudin fansa, 'yan ta'adda kuwa na kashe mutane ne da muhallansu a jihohin.

4. Fadan ƙabilanci

Akan abin da ya shafi rikicin kabilanci da muhalli kuwa, jihohin Filato, Nasarawa, Taraba da Benue ne suka fi fama da wannan matsalar a cewar Sanata Sani.

5. Fadan ƙabilanci da harin 'yan ta'adda

Jihohin Filato, Kaduna da Nasarawa su ma na fama da rikicin kabilanci da hare-haren 'yan ta'adda.

Yayin da mazauna garuruwan ke fada da junansu kan muhalli, a hannu daya kuma 'yan ta'adda sun hana su zama sakat.

6. Rikicin manoma da makiyaya

Benue, Filato, Kaduna, Taraba, Nasarawa, su ne jihohin da suka fi fama da rikicin manoma da makiyaya.

Hakan ya fi ƙamari musamman idan lokacin damina ya zo zuwa lokacin girbi. Wannan rikicin ya salwantar da rayuka da dama.

7. Rikicin kabilanci da addini

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamnan LP ya biya bashin da matarsa ta ci bayan an sha yar dirama a Twitter

Idan ana maganar fadan kabilanci hade da na addini a Arewa, to ana maganar jihohin Kadunaz Filato, Nasarawa da Adamawa ne.

Akwai mabiya addinai daban daban a wadannan jihohi wadanda kuma ke rayuwa a waje daya, sai dai kullum suna cikin zaman dar-dar saboda fargar hari daga wani bangare.

Duba wallafar da tsohon sanatan ya yi a kasa:

Taraba: Yan bindiga sun kai hari kan 'yan gudun hijira

A wani labarin, wasu gungun mayaka dauke da makamai da ake zargin 'yan kabilar Jukun ne, sun kashe wasu 'yan gudun hijira a Ikyenum, karamar hukumar Wukari da ke Taraba.

An ruwaito cewa, 'yan gudun hijirar na kan hanyar komawa gida lokacin da 'yan bindigar suka tare su, suka bude wuta kan duk wanda suka gani, sun kashe mutum biyu nan take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel