Sheikh Gumi: Yakar Yan Ta’adda da Makaman Yakin Duniya II Tsohon Yayi Ne

Sheikh Gumi: Yakar Yan Ta’adda da Makaman Yakin Duniya II Tsohon Yayi Ne

  • Sheikh Ahmad Gumi ya ce kashe biliyoyin naira wajen siyo makaman da aka yi su a Yakin Duniya II don yaki da 'yan ta'adda tsohon yayi ne
  • A cewar malamin addinin kuma tsohon soja, lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta zauna a teburin tattaunawa da 'yan bindiga
  • Sheikh Gumi ya ce bunkasa aikin 'yan sanda zai iya kawo karshen ta'addancin cikin gida ba wai a sakarwa sojoji ragamar hakan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce kashe biliyoyin nairori wajen siyan makamai ba zai kawo karshen yaki da 'yan ta'adda ba.

Sheikh Gumi a zantawarsa da gidan talabijin na Trust, ya ce ya kamata gwamnati ta dauki matakin tattaunawa wajen magance matsalar tsaro, ba wai amfani da makamai kadai ba.

Kara karanta wannan

Rundunar Sojojin Najeriya ta kama jami’inta kan mutuwar direban babban mota a Borno

Dr Ahmed Gumi ya fadi hanyoyin murkushe 'yan ta'adda
Dr Ahmad Gumi ya ce kashe biliyoyin nairori wajen siyan makamai ba zai kawo karshen yaki da 'yan ta'adda ba. Hoto: @AAGummi
Asali: Facebook

Ya ce 'yan bindiga sun samo asali ne daga rikicin manoma da makiyaya a Arewacin kasar, inda ya ke ganin tattauna da 'yan bindigar zai kawo karshen hare-hare a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Sheikh Gumi ya ce kan ayyukan sojojin Najeriya

Da ya ke magana kan harin da sojoji suka kai Tudun Biri a jihar Kaduna, tsohon sojan ya ce lokaci ya yi da ya kamata sojoji su daina tsoma baki a tsaron cikin gida.

Ya ce yanzu lokaci ne da ya kamata a bunkasa rundunar 'yan sanda domin magance matsalar hare-haren 'yan bindiga, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar malamin addinin:

"Ba wannan ne karon farko da hakan ta faru ba. Ya kamata ace sojoji na can suna yaki da 'yan ta'adda, amma jefa bama-bamai a kan farar hula da sunan farmakar 'yan ta'adda zance ne kawai.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya fallasa babbar matsala da ke kara rura wutar hare-haren 'yan bindiga a Arewa

"Da ace wani shugaban kasar Amurka ne, jirgin sojin kasar ya kai irin wannan harin kan 'yan Amurka, ina tabbatar maka washe gari zai sauka daga mulki, saboda ba sa wasa da hakan."

A tattauna da 'yan bindiga, shi ne maslaha - Sheikh Gumi

Ya ci gaba da cewa:

"Duk kudin da ake kashewa wajen siyo makamai da jiragen yaki, tsohuwar dibara ce ta yaki da 'yan ta'adda, a zo a zauna da mutanen nan, aji matsalarsu tare da kawo karshen abin.
"Muna sane da cewa ko su wadanda muke kira 'yan bindiga, sun yi korafin cewa an lalata kasuwancin dabbobinsu, an tarwatsa muhallansu."

A karshe Sheikh Gumi ya ce ma damar Najeriya na son kawo karshen ta'addanci, dole sojoji su koma bakin boda, a bar 'yan sanda su ji da matsalar tsaron jihohi.

Harin sojoji a Tudun Biri ganganci ne ba kuskure ba - Sheikh Gumi

Sheikh Ahmad Gumi ya yi Allah wadai da harin sojoji a garin Tudun Biri, jihar Kaduna, inda ya ce harin ganganci ne ba wai kuskure ba kamar yadda sojojin suke ikirari.

Kara karanta wannan

Ba Dani Ba: Sheikh Dahiru ya yi martani kan wasikar da aka ce ya rubuta kan rikicin Abba da Gawuna

A wani bayani da ya fitar a shafinsa na Facebook, malamin addinin ya ce abin takaici ne yadda 'yan ta'adda ke kashe mutane, yanzu kuma sojoji su ma suna kai wa farar hula hari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel