Katsina: Yan Bindiga Sun Afka Sansanin Sojoji, Sun Tafka Barna Tare Da Mamaye Wani Kauye

Katsina: Yan Bindiga Sun Afka Sansanin Sojoji, Sun Tafka Barna Tare Da Mamaye Wani Kauye

  • Wasu 'yan bindiga dauke da manyan makamai da suka hada da AK-47 sun farmaki sansanin jami'an tsaro a jihar Katsina
  • Farmakin wanda aka kai a ranar Lahadi, an ruwaito jami'an tsaron sun fatattaki 'yan bindigar duk da sun fi su yawa
  • Sai dai wata majiya ta shaida cewa 'yan bindkgar sun shiga kauyen Nahuta, inda suka fasa shaguna da gidaje suka tabka sata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Katsina - Gungun 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun farmaki wani sansanin jami'an tsaro a kauyen Nahutu da ke karamar hukumar Batsari, jihar Katsina.

Wata majiya ta shaidawa jaridar Channels TV cewa 'yan bindigar sun kai harin a ranar Lahadi, kuma sun lalata motoci da wasu kayayyaki yayin kai farmakin.

Kara karanta wannan

An kashe yan bindiga yayin da suka yi yunkurin kai hari a arewa

Yan bindiga sun farmaki sansanin sojoji a Katsina
Yan bindiga sun farmaki sansanin sojoji a Katsina, sun tafka barna. Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Jami'an tsaro sun dakile harin 'yan bindigar

Duk da cewa ba ayi asarar rayuka ba, amma jaridar ta rahoto cewa jami'an tsaron a sansanin sun dakile harin duk da cewa 'yan bindigar sun fi su yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar majiyar:

"Yan bindigar sun fi mu yawa kuma sun mamaye sansanin na mu tare da cinnawa motoci da kayayyakin mu wuta, ba a kawo mana dauki har muka fatattake su."

Yan bindiga sun yi sata a kauyen Nuhuta

Sai dai 'yan bindigar sun yi amfani da wannan damar wajen kai farmaki kauyen Nahuta, inda suka fasa shaguna da gidaje tare da sace kayayyaki da dabbobi na makudan kudade.

Har zuwa rubuta wannan rahoton, babu wani jawabi daga jami'an tsaro kan wannan farmaki da aka kai jihar da ke Arewa maso Yamma.

Jihar Katsina dai na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da hare-haren 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka mummunar ɓarna, sun sace mata sama da 35 tare da kashe rayuka a arewa

Ko a makon da ya gabata sai da jaridar Leadership ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kashe mutum takwas da ke kan hanyar komawa gida daga kasuwar Yantumaki da ke Danmusa a jihar.

Yan ta'adda sun datse hannun masunta a jihar Borno

A wani labarin kuma, 'yan ta'addan ISWAP sun datse hannun wasu masunta biyu a garin Marte da ke jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yanke hukuncin ne bayan sun kama masuntan da laifin sun yi masu satar kifi har kwando biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel