Sarkin Kano
Za a ji cewa amsa ta fito a kan wanene sahihin Sarkin Kano ta fuskar doka. Barista Abba Hikima ya ce har gobe Aminu Ado Bayero yana kan karagar mulki.
Fitaccen lauya a jihar Kano, Abba Hikima ya bayyana sahihin sarkin Kano bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya kan sarautar da aka yanke a jiya Alhamis.
Gwamnatin Kano na ci gaba da shirye-shiryen rusa wani ɓangaren fadar Nassrawa wadda Sarki na 15, Aminu Ado Bayero ke ciki, an ga buldoza ta kama hanya.
Kungiyar Lauyoyi a Arewacin Najeriya (NCNLPIA) ta yi martani kan hukuncin kotu kan masarautun jihar inda ta bukaci Abba Kabir ya ba Aminu Ado Bayero hakuri.
Har yanzun dai ana ci gaba da takun saƙa tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero duk hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke jiya Alhamis.
Dubban masoya sun tarbi Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yayin dawowa daga sallar Juma'a da kuma kai gaisuwa fadar Nassarawa kwana daya da yanke hukunci.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano ya ce gwamnati za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotu ta yanke na soke matakin mayar da Muhammadu Sanusi II.
Wata kungiya a Arewa ta gargadi gwamnan Kano kan bijirewa umurnin kotu bayan yanke hukunci tsakanin Sanusi II da Aminu Ado Bayero a jiya Alhamis.
Bayan umarnin tuge Aminu Ado daga fadar Nassarawa, Kwamishinan ƴan sanda a jihar Kano, Hussaini Gumel ya yi martani kan umarnin inda ya ce ba za su bi umarnin ba.
Sarkin Kano
Samu kari