Bayan Yanke Hukunci, an Yaɗa Bidiyon Yadda Dubban Kanawa Suka Cika Fadar Aminu Ado

Bayan Yanke Hukunci, an Yaɗa Bidiyon Yadda Dubban Kanawa Suka Cika Fadar Aminu Ado

  • Yayin da ake cigaba da dambarwa kan rigimar sarautar Kano, Aminu Ado Bayero ya samu tarba daga dubban masoya
  • Yayin da yake dawowa daga sallar Juma'a, dubban Kanawa ne suka tarbi Sarkin a birnin Kano a yau 21 ga watan Yunin 2024
  • Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan rigimar da ake yi kan sarautar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kwana daya bayan yanke hukunci kan dambarwar sarautar Kano, Aminu Ado Bayero ya samu tarba daga dandazon jama'a.

Dubban masoya ne suka cika fadar Aminu Ado domin gaisuwar Juma'a a yau 21 ga watan Yunin 2024.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Lauyoyin Arewa sun yabawa hukuncin kotu, sun gargaɗi gwamna Abba

Dubban Kanawa sun tarbi Aminu Ado Bayero a Kano
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya samu tarba ta musamman daga dubban Kanawa. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Kano: Aminu Ado da soyayyar Kanawa

A cikin wani faifan bidiyo da Masarautar Kano ta wallafa a shafin X, an gano yadda dubban masoya ke murna da ganin Aminu Ado.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, masoya Sarkin Kano na 15 sun yi ta ihun cewa "Sai ka yi" yayin da yake dawowa daga masallacin Juma'a a yau.

Aminu v Sanusi: Hukuncin da kotu ta yi

Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan yanke hukunci kan rigimar sarautar Kano a jiya Alhamis 20 ga watan Yunin 2024.

Babbar Kotun Tarayya ta yi fatali da duka matakan da Gwamna Abba Kabir ya dauka wurin aiwatar da dokar masarautun guda biyar.

Ta tabbatar da cewa dokar rusa masarautun jihar guda biyar a watan Mayun 2024 tana nan daram ba tare da matsala ba.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun aikawa Gwamna Abba amsar umarnin tuge Aminu Ado daga fadar Nassarawa

Mai shari’a Abdullahi Liman ya ce Gwamna Abba Yusuf ya yi biris da umarnin hana mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarki.

Ƴan sanda sun yiwa Abba Kabir martani

Kun ji cewa Kwamishinan ƴan sanda a jihar Kano, Hussaini Gumel ya yi martani kan umarnin fitar da Aminu Ado daga fadar Nassarawa.

Gumel ya ce ba za su bi umarnin gwamnan ba tun da gwamnatin ta shigar da korafi a babbar kotun jihar kan lamarin.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya umarci kwamishinan ya fitar da Aminu Ado daga fadar Nassarawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.