Kano: Farfesa Ya Fadi Yadda Abba Zai Yi Nasara, Ya Magantu Kan Rusa Fadar Nassarawa

Kano: Farfesa Ya Fadi Yadda Abba Zai Yi Nasara, Ya Magantu Kan Rusa Fadar Nassarawa

  • Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan masarautun Kano, Farfesa Farooq Kperogi ya yi tsokaci kan lamarin
  • Kperogi ya zargi Shugaba Bola Tinubu da tsoma baki cikin rikicin wanda ya kara rikita lamarin da kawo barazana
  • Farfesan ya kuma shawarci Gwamna Abba Kabir da ya bar shari'a ta yi aikinta inda ya gargade shi kan rushe fadar Nassarawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Farfesa Farooq Kperogi ya magantu kan rikicin sarautar jihar Kano da ake ciki yanzu.

Kperogi ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta nuna girma wurin ba bangaren shari'a yin hukuncin da ya dace.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abba Hikima ya magantu kan sahihin Sarkin Kano, ya jero dalilai

Farfesa ya yi tsokaci kan rigimar sarautar Kano, ya ba Abba Kabir shawara
Farfesa Farooq Kperogi ya shawarci Abba Kabir kan rushe fadar Nassarawa. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Kabir Yusuf, Masarautar Kano.
Asali: UGC

Kano: Kperogi ya zargi Tinubu kan rigimar

Farfesan ya bayyana haka ne a rubutunsa na mako-mako da ya wallafa a shafin X a yau Asabar 22 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya zargi Shugaba Bola Tinubu da tsoma baki a lamarin sarautar jihar inda ya ce hakan kwata-kwata bai dace ba.

Ya ce hakan kara rikita lamura ya ke yi madadin shawo kan matsalolin da ake fuskanta a jihar.

Kperogi ya shawarci Abba kan fadar Nassarawa

"Gwamnatin Tarayya ba ta da ikon shiga lamarin sarauta a kowace jiha a ƙasa, Femi Falana ma ya ce manyan kotunan Tarayya ba su da ikon daukar mataki kan abin da ya shafi masarautu."
"Ya kamata gwamnatin jihar Kano ta girmi wannan lamari ta bar bangaren shari'a ta yi abin da ya ce."
"Rushe gidan Aminu Ado Bayero ba abu ne mai kyau ba, ba na tare da hakan amma kamar rusau ya bi jinin jikin gwamnan."

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Lauyoyin Arewa sun yabawa hukuncin kotu, sun gargaɗi gwamna Abba

- Farooq Kperogi

Abba Hikima ya magantu kan masarautun Kano

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen lauya a Kano, Abba Hikima ya yi tsokaci kan rigimar sarautar jihar da ake ciki.

Hikima ya ce a mahangar shari'a a yanxu Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano duba da hukuncin kotu kan rigimar.

Wannan na zuwa ne bayan Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci da wasu fitattun lauyoyi ke ganin akwai sarkakiya a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.