‘Burgar banza’: Hadimin Ganduje Ya Takalo Abba Kan Yunkurin Fatattakar Sarki Aminu

‘Burgar banza’: Hadimin Ganduje Ya Takalo Abba Kan Yunkurin Fatattakar Sarki Aminu

  • Salihu Tanko Yakasai bai ganin cewa gwamnatin jihar Kano za ta iya ruguza karamar fadar Sarki da ke Nassarawa
  • Tsohon ‘dan takaran gwamnan ya zargi gwamna Abba Kabir Yusuf da yawan nuna kunnen kashi ga umarnin alkalan kotu
  • Salihu Tanko Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu ya ce an karawa Sarki Aminu Ado Bayero jami’an tsaro a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Salihu Tanko Yakasai ya yi aiki a gidan gwamnatin Kano, ya na cikin masu tofa albarkacin bakinsu kan halin da ake ciki.

Ana ta kai ruwa rana a game da sarautar Kano tun bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya sa hannu a doka, ya ruguza masarautu.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya ja kunnen Abba kan yunkurin ruguza fadar Aminu a Nassarawa

Aminu Ado Bayero
Gwamnan Kano na kokarin raba Aminu Ado Bayero da Fadar Nassarawa Hoto: @KYusufAbba/@HRHBayero
Asali: Twitter

Gwamnan Kano zai rusa fadar Nassarawa

Salihu Tanko Yakasai ya yi magana a shafin X bayan an ji Mai girma Abba Kabir Yusuf yana kokarin ruguza fadar da ke Nassarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan siyasar ya yi martani yana mai cewa barazanar banza kurum gwamnan na Kano yake yi, babu yadda ya iya da karamar fadar.

Zargin gwamna Abba da sabawa kotu

Hadimin na Abdullahi Umar Ganduje ya zargi gwamnatin Abba da saba umarnin kotu.

A baya an ji yadda alkali Abdullahi Muhammad Liman ya zargi gwamnatin NNPP da bijire masa wajen nada Muhammadu Sanusi II.

Gwamna ya sa an kara tsaro a Nassarawa

"A daren jiya, aka kara tsaro sosai a fadar Nassarawa domin ba Sarki Aminu kariya a sakamakon barazanar kurum da gwamnatin jihar Kano ta yi,"

Kara karanta wannan

Lauya ya ci gyaran gwamna, ya fassara hukuncin Alkali a shari’ar masarautar Kano

"Inda ta yi gigin rusa fadar (Nassarawa), duk da umarnin kotu cewa kowa ya dakata da batun."
"Wannan ma wani misalin yiwa kotu karon tsaye ne wanda ya zama ruwan dare a gwamnatin nan."

- Salihu Tanko Yakasai

A karshe Yakasai ya ba Abba shawarar cewa a matsayin gwamna, kyau ya zagaye kan shi da wadanda suka san abin da ya dace.

Bashir Ahmaad ya ba Gwamna Abba shawara

Ku na da labarin ana zargin Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta na neman cire Aminu Ado Bayero daga fadar Nassarawa da kafi da yaji.

Bashir Ahmaad ya ba gwamnan Kano shawarar ya daina tunanin amfani da kudin jama'a wajen ruguza fadar da Sarki na 15 yake zaune.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng