Sanusi II vs Aminu Ado: Shehu Sani Ya Kawo Hanyar Warware Rikicin Sarautar Kano

Sanusi II vs Aminu Ado: Shehu Sani Ya Kawo Hanyar Warware Rikicin Sarautar Kano

  • Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda zaɓe zai warware rikicin masarautar Kano da ke faruwa tsakanin sarakunan Kano Muhammad Sanusi II da Aminu Ado Bayero
  • A cikin wani rubutu na raha, Shehu Sani ya ce ya kamata a gayyato hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gudanar da zaɓen a tsakanin sarakunan biyu
  • Tsohon Sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya sadaukar da kansa domin yin aiki a matsayin jami'in zaɓe a zaɓen na masarautar Kano

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja- Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ba da shawara kan hanyar warware rikicin masarautar Kano.

Shehu Sani ya ce ya kamata a gayyaci hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) domin gudanar da zaɓe ta yadda za a warware rikicin da ke tsakanin Muhammad Sanusi II da Aminu Ado Bayero.

Kara karanta wannan

"Ba a sauke Sanusi II ba," Gwamnatin Kano ta yi ƙarin haske kan hukuncun kotu

Shehu Sani ya yi magana kan sarautar Kano
Shehu Sani ya ba da shawara a yi zabe kan rikicin sarautar Kano Hoto: Sanusi Lamido Sanusi/@Super_Joyce/@ShehuSani
Asali: UGC

Muhammad Sanusi II da Aminu Ado Bayero dai sun samu kansu a cikin rikicin masarautar Kano biyo bayan sabuwar dokar da majalisar dokokin jihar ta yi kan masarautun jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Shehu Sani ya ce kan rikicin sarautar Kano?

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X, Shehu Sani ya ce kamata ya yi a gayyaci hukumar zaɓe domin warware taƙaddamar da ke tsakanin sarakunan biyu.

Ya ce zai yarda ya yi aiki a matsayin jami’in zaɓe a zaɓen kuma za a iya amfani da na'urar Bivas.

Tsohon Sanatan na Kaduna ta tsakiya ya yi wannan rubutun ne na raha a ranar Juma'a, 21 ga watan Yunin 2024.

A cikin rubutun nasa na barkwanci, Shehu Sani ya ƙara da cewa ana iya amfani da na'urar tantance masu kaɗa ƙuri’a (BIVAS) a lokacin zaɓen.

Kara karanta wannan

Kano: Yadda Sanusi II da Aminu Bayero suka yi Sallar Jumu'a bayan hukuncin kotu

"Kawai a gayyaci INEC domin gudanar da zaɓe a tsakanin sarakunan biyu masu taƙaddama, zan iya yarda na zama jami’in zaɓe a kyauta. Ana iya amfani da Bivas."

- Shehu Sani

Sahihin Sarkin Kano a yanzu

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen lauya a jihar Kano, Abba Hikima ya yi martani kan dambarwar sarautar Kano bayan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yi.

Lauyan ya ce a yanzu sahihin Sarkin Kano a mahangar doka shi ne Aminu Ado Bayero saboda kotu ta yi fatali da matakan Gwamna Abba Kabir ya ɗauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng