Kano: Yadda Sanusi II da Aminu Bayero Suka Yi Sallar Jumu'a Bayan Hukuncin Kotu

Kano: Yadda Sanusi II da Aminu Bayero Suka Yi Sallar Jumu'a Bayan Hukuncin Kotu

  • Muhammadu Sanusi II ya jagoranci Sallar Jumu'a a babban Masallacin fadar Ƙofar Kudu duk da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke
  • Haka nan kuma Aminu Bayero ya yi Sallah a ƙaramar fadar Nasarawa, sarakunan sun yi zaman fada yau Jumu'a, 21 ga watan Yuni, 2204
  • Jiya Alhamis kotu ta soke matakin mayar da Sanusi II kan karagar sarauta saboda take umarninta da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya gudanar da zaman fada kamar yadda aka saba a fadar Sarki da ke Ƙofar Kudu yau Jumu'a.

Sanusi II wanda babbar kotun tarayya ta soke matakin dawo da shi kan sarauta, ya jagoranci Sallar Jumu'a a babban Masallacin fada yau 21 ga watan Yuni, 2024.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Shehu Sani ya kawo hanyar warware rikicin masarautar Kano

Muhammadu Sanusi da Aminu Bayero.
Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II sun yi Sallar Jumu'a fadar da kowane ke zaune duk da hukuncin kotu Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Facebook

Yadda Aminu Bayero ya yi zaman fada

A ɗaya ɓangaren kuma shi ma Sarki na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi zaman fada a ƙaramar fadar Sarki da ke Nassarawa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma Aminu Bayero ya yi Sallar Jumu'a a cikin jam'i a Masallacin ƙaramar fadar da yake ciki duk da ana raɗe-raɗin gwamnatin Kano za ta yi gyara.

Sai dai rahotanni sun ce an kara girke jami'an tsaro a ƙaramar fadar Nasarawa, inda Aminu Bayero ke ciki bayan sanarwar shirin gwamnati na rusa wani sashi.

An tsaurara tsaro a fadar Nassarawa

Jami'an tsaro cikin shirin ko ta kwana sun taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a titin da ke baya da na gefen fadar, sun mamaye hanyar shiga da fita daga ƙaramar fadar.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da suka faru da Sanusi II tun da ya koma karaga a tsakiyar rikicin sarauta

Wannan dai na zuwa ne bayan babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta soke matakin Abba na tuɓe Aminu Ado Bayero da kuma naɗa Sanusi II a matsayin Sarki.

Mai Shari'a Liman ya ce hukuncin kotun bai shafi dokar masarauta ta 2024 wanda majalisar dokokin jihar ta amince da ita ba.

Bayan hukunci ne gwamnatin Kano ta umarci kwamishinan ƴan sanda ya ɗauke Aminu Ado daga fadar da yake ciki saboda tana shirin yin wasu gyare-gyare, Channels tv ta ruwaito.

Mazaunin Kano kuma mamban NNPP, Sanusi Isiyaku, ya shaida mana cewa ya bi ta Nasarawa da yammacin ranar Jumu'a kuma ya ga motocin ƴan sanda kusan 10.

A kalamansa ya ce:

"Na ga motocin ƴan sanda da sojoji za su kai 10 a wurin suna gadin Aminu Ado, ni abin da ke ƙara ɗaure mun kai, gwamna shi ne shugaban tsaro a jiharsa amma idan ya yi magana ba a masa biyayya.

Kara karanta wannan

Bayan yanke hukunci, an yaɗa bidiyon yadda dubban Kanawa suka cika fadar Aminu Ado

"Tun da ya ce zai rushe katangar Nasarawa saboda ta tsufa suka firgita, suka ƙara yawan jami'an tsaro. Mu dai bamu fasa harkokinmu ba, Allah ya kawo mana ƙarshen abun."

Gwamna Abba zai ɗaukaka ƙara a kotu

A wani rahoton na daban Gwamnatin Kano karƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin soke naɗin Muhammadu Sanusi II.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Alhaji Baba Ɗantiye ne ya tabbatar da haka a wani saƙo da ya turawa manema labarai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262