Kungiyar Arewa Ta Yi Matsaya Bayan Shari’ar Kano, Ta Gargadi Abba Kan Tayar da Fitina

Kungiyar Arewa Ta Yi Matsaya Bayan Shari’ar Kano, Ta Gargadi Abba Kan Tayar da Fitina

  • Al'ummar Najeriya na cigaba da tofa albarkacin baki biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke a jiya Asabar kan rikicin sarautar jihar Kano
  • Wata kungiya a Arewacin Najeriya ta nuna farinciki kan yadda aka gudanar da shari'ar cikin nasara tare da jinjinawa alkalin kotun
  • Kungiyar ta kuma tura sakon gargadi ga gwamna jihar Kano Abba Kabir Yusuf kan kaucewa tayar da fitina bayan shari'ar ta gudana

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - A jiya Alhamis ne alkalin kotun gwamnatin tarayya da ke Kano ya yanke hukunci kan rikicin sarautar jihar Kano.

Biyo bayan hukuncin, wata kungiya a Arewa (FCN) ta bayyana farin ciki kan yadda kotun ta yi watsi da matakin da gwamnatin jihar ta dauka.

Kara karanta wannan

"Akwai rikitarwa": Farfesan Lauyoyi, Yadudu ya gano kuskure a hukuncin shari'ar sarautar Kano

Masarautar Kanao
Kungiyar FCN ta goyi bayan Aminu Ado Bayero. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa kungiyar ta tura sakon gargadi ga gwamna Abba Kabir Yusuf kan kada ya kara jawo wani rikici bayan hukuncin da kotun ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

FCN: 'Kotu ta yi adalci'

Kungiyar FCN ta ce kotun ta yi adalci wajen rusa dawo da Muhammadu Sanusi II kan karagar mulkin jihar Kano.

Har ila yau kungiyar ta ce wannan kuma nasara ce ga daukacin al'umma saboda gaskiya ce ta yi nasara kan karya.

FCN ta kara da cewa alkallin ya nuna hikima da jajircewa kan kin yadda ya aikata zalunci a cikin shari'ar, rahoton Pulse Nigeria.

Kungiyar FCN ta gargadi gwamna Abba

A cikin sakon da kungiyar ta fitar, ta yi kira na musamman ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf kan yarda da hukuncin kotun.

FCN ta ce bai kamata gwamnan ya dauki wani matakin da zai kawo rashin zaman lafiya a jihar ba, ya kamata kawai ya sallama ga hukuncin da kotun ta yi.

Kara karanta wannan

Hukumar kwastam za ta dauki matakin da zai kawo saukin kayan abinci a Najeriya

Ta kara da cewa duk wani abu da ya taso a jihar bayan gwamnan ya dauki matakin tabbatar da Muhammadu Sanusi II kan mulki to alhaki zai koma kansa.

Abba zai rusa fadar Aminu Bayero

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta umarci kwamishinan 'yan sanda ya fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado daga fadar Nasarawa.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya ba da wannan umarni domin fara gyara a wasu bangarori na fadar da ke Kano ba tare da bata lokaci ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng