Lauya Ya Ci Gyaran Gwamna, Ya Fassara Hukuncin Alkali a Shari’ar Masarautar Kano

Lauya Ya Ci Gyaran Gwamna, Ya Fassara Hukuncin Alkali a Shari’ar Masarautar Kano

  • Abba Hikima ya yi fashin bakin hukuncin da Alkali Abdullahi Muhammad Liman ya yi a shari’ar masarautar Kano
  • Lauyan ya ce a fuskar doka, har gobe Mai martaba Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano ba Muhammadu Sanusi II ba
  • Hikima ya kuma shaidawa jama’a cewa masarautun da Abba Kabir Yusuf ya rusa suna nan duk da an kori sarakunan

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Abba Hikima fitaccen lauya ne wanda ya shahara musamman a jihar Kano wajen kare masu karamin karfi da fadan gaskiya.

Barista Abba Hikima ya yi bayani game da hukuncin da kotun tarayya ta yi a karkashin Muhammad Liman a kan masarautar Kano.

Sarkin Kano
Ana shari'a kan sarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero Hoto: @HRHBayer/Ibrahim Sanyi-Sanyi
Asali: Twitter

Lauya Abba Hikima ya fassara hukuncin kotu

Kara karanta wannan

‘Burgar banza’: Hadimin Ganduje ya takalo Abba kan yunkurin fatattakar Sarki Aminu

Lauyan ya bayyana ra’ayinsa ne a wani matsakaicin bidiyo da ya dauka kai-tsaye a shafinsa na Facebook a safiyar Juma’ar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Hikima ya ce ya zama dole ya yi bayanin ne ganin yadda jaridu da gidajen yada labarai su ka rika juya hukuncin alkalin kotun.

Abba Hikima ya sabawa Gwamnatin Kano

A ra’ayin Hikima, hukuncin da kotu ta fara zartarwa yana nufin har yanzu Aminu Ado Bayero ne sarki ba Muhammadu Sanusi II ba.

Baya ga haka, lauyan ya ce hukuncin ranar Alhamis da alkali ya yi ya tabbatar da cewa har yanzu ba a ruguza masarautu biyar ba.

Dalilinsa na cewa haka kuwa shi ne alkali ya umarci duka bangarorin da ake shari’a da su, su koma yadda ake kafin kawo dokar 2024.

Kotu ta jingine dokar masarautun Kano

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu: Hadimin gwamna da fitaccen lauya sun samu saɓani kan hukuncin kotu

Shakka babu, alkali Muhammad Liman bai yi jayayya da ingancin dokar masarautun Kano na 2024, amma ya yi umarni a tsaida aiki da ita.

Duk da dokar ba ta haramta ba, Hikima ya ce alkali ya wajabta dakatar da aiki da ita kuma har yanzu bai janye wannan dakatarwa ba.

Idan kotu ta ba da umarni, ko da ba daidai ba ne, masanin shari’ar ya ce dole ne a yi biyayya, idan ta gama daga baya a hukunta alkalin.

Lauyan ya maimaita haka da aka yi hira da shi a Channels, sai dai masanin shari’ar ya ce watakila za a iya samun wanda ya saba da shi.

Yaron Sarki Sanusi II ya yi magana

Ana da labarin cewa Ashraf Sanusi Lamido Sanusi ya fadi ra'ayinsa da ake shari'a a kotun tarayya game da sarautar jihar Kano.

Malam Ashraf Lamido Sanusi ya ce ba a taka hakkin Aminu Ado Bayero wajen cire masa rawani ba domin dama sarauta gata ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng