Hukumar yan sandan NAjeriya
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kutsa cikin dakin kwanan dalibai na jami'ar Calabar (UNICAL), inda suka yi awon gaba da wasu mutum uku yayin harin.
Yayin da ake ci gaba da azumin watan Ramadan, 'yan sanda sun cafke wani malamin Musulunci, Alfa Oluwafemi Idris da sassan jikin ɗan Adam a jihar Ondo.
An samu tashin wani abun fashewa a jihar Taraba wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum hudu. Wasu mutane da dama kuma sun samu munanan raunuka.
Rahotanni daga kauyen Dawaki da ke karamar hukumar Bwari a Abuja ya nuna cewa wani da ba a tantance ko menene ba ya fashe a ɗakin wasu mutum 2 ranar Jumu'a.
An bayyana yadda 'yan sanda suka kai ga kame wadanda suka kashe 'yan sanda shida a jihar Delta a makon da ya gabata. An bayyana yadda aka kama su.
'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari cikin cocin Celestial da ke jihar Ogun inda suka sace mambobin cocin su na tsaka da gudanar da bauta a kauyen Oriyarin.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Delta ta tabbatar da cewa ta miƙa sarkin Ikolo ga rundunar sojoji bayan ya miƙa kansa kan zargin hannu a kisan sojoji 17 a Okuama.
Mai Martaba Clement Oghenerukevwe Ikolo, Urhukpe 1, ya mika kansa ga ‘yan sandan jihar Delta, bayan da aka alakanta shi da sa hannu a kashe sojojin Najeriya.
Dakarun rundunar ƴan sandan jihr Benuwai sun yi nasarar halaka ƴan bindiga 2 yayin musayar wuta a karamar hukumar Katsina Ala, sun damƙe mutum ɗaya.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari