Gwamnatin Zamfara Ta Dauki Muhimmin Mataki Don Kawo Karshen 'Yan Bindiga

Gwamnatin Zamfara Ta Dauki Muhimmin Mataki Don Kawo Karshen 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta ɗauki matakin haramta sayar da man fetur a jarkoki ga masu motoci da babura a jihar
  • Kwamishinan yaɗa labarai da al'adu na jihar wanda ya sanar da hakan ya ce haramcin ya haɗa har da sayar da biredi
  • Ya bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne biyo bayan gano yadda wasu gidajen mai da gidajen biredi ke sayar da kayayyakinsu ga ƴan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da hana sayar da biredi da man fetur a jarkoki ga masu motoci da masu tuƙa babura saboda dalilai na tsaro.

Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Mannir Muazu Haidara ya bayyana haka a taron manema labarai a ƙarshen taron majalisar tsaro na jihar, cewar rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu: An tsaurara tsaro a Kano kan abu 1 tak

Gwamnatin Zamfara ta hana sayar da man fetur a jarkoki
Gwamnatin Zamfara ta bankado masu sayar da man fetur ga 'yan bindiga Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Meyasa gwamnatin Zamfara ta ɗauki matakin?

Haidara ya ce majalisar ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon munanan ayyuka da wasu gidajen mai, da ke da ɗabi’ar sayar da mai a jarkoki da biredi ga wasu da ake zargin ƴan bindiga ne a wasu ƙauyukan jihar, rahoton DailyPost ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Majalisar ta lura cikin takaici da yadda wasu gidajen mai da gidajen biredi da kuma masu sayar da biredi a wasu yankunan karkara ke amfani da motoci da babura wajen sayar da man fetur da biredi ga wasu da ake zargin ƴan bindiga ne. Muna shawartarsu da su daina aikata hakan.

Ya kuma ƙara nanata cewa majalisar ta haramta amfani da baƙin gilashi, ɓoyayyiyar lamba da amfani da jiniya ba tare da izni ba, tare da umurtar jami’an tsaro da su kama masu aikata hakan da kuma gurfanar da su gaban kuliya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Arewa, sun sace gomman mutane

Gwamnati ta shawarci masu ababen hawa

Haidara ya shawarci masu ababen hawa da har yanzu ba su yi rajistar lambobin motocinsu ba, da su yi hakan ba tare da ɓata lokaci ba, domin an ba hukumomin da abin ya shafa da jami’an tsaro damar kamawa tare da gurfanar da waɗanda ba su yi hakan ba a gaban kuliya.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, jami’an tsaro sun ƙwato wasu shanu daga hannun ƴan bindiga.

Sannan ya yi kira ga mutanen da aka sace shanunsu da su zo da hujjojin da suka dace domin karɓar dabbobinsu da aka sace bayan sun bi ƙa'idar da ta dace.

Gwamna Dauda Ya Ƙaddamar da Asusun Tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya ƙaddamar da hukumar asusun tsaro na jihar Zamfara.

Gwamnan ya kuma naɗa tsohon sifetan ƴan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar a matsayin shugaban sabuwar hukumar asusun tsaro a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel