Innalillahi: Mahara Sun Hallaka Jami'an ’Yan Sanda 2 da Sace Fiye da 40 a Sabon Hari a Zamfara

Innalillahi: Mahara Sun Hallaka Jami'an ’Yan Sanda 2 da Sace Fiye da 40 a Sabon Hari a Zamfara

  • An shiga tashin hankali bayan ‘yan bindiga sun hallaka jami’an ‘yan sanda biyu tare da sace mutane 40 a harin
  • Lamarin ya faru ne da safiyar yau Talata 13 ga watan Faburairu a kauyen Kasuwar-Daji a karamar hukumar Kaura Namoda
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani mazaunin garin Kasuwar-Daji inda ya tabbatar da faruwar lamarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga sun hallaka jami’an 'yan sanda biyu da sace wasu mutane 40 a jihar Zamfara.

Harin ya faru ne a kauyen Kasuwa Daji a karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar.

'Yan sanda 2 sun rasa ransu yayin da aka sace mutane 40
Yan Bindiga Sun Hallaka Jamia’n ’Yan Sanda 2 da Sace Mutane 40 a Zamfara. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Yaushe aka kai harin a Zamfara?

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan daba suka farmaki kwamishina a jihar Arewa, sun sace motarsa

Mazauna yankin sun tabbatar da cewa maharan sun durfafi kauyen ne da safiyar yau Talata 13 ga watan Faburairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels TV ta tabbatar da cewa maharan na dauke da muggan makamai hade da makamin kakkabo jirgin sama.

Majiyar ta ce maharan sun kuma kai hari gidan tsohon shugaban kungiyar NURTW, Hamisu Kasuwar-Daji inda suka sace matarsa da jikokinsa.

An tabbatar da cewa gidan Hamisu na kusa da ofishin ‘yan sanda inda suka farmaki ofishin tare da hallaka jami’ai biyu da dauke makamansu.

Har ila yau, wani mazaunin yankin da ya bukaci a boye sunansa ya ce maharan sun kuma hallaka wasu mutane biyu yayin kai harin, cewar Politics Today.

Ya tabbatar da cewa akalla mutane 40 aka sace yayin kai harin da maharan suka yi gida-gida.

Legit Hausa ta ji ta bakin wani mazaunin garin Kasuwar-Daji, Mustapha Kasuwar-Daji kan harin.

Kara karanta wannan

An ji kunya: Matasa masu karfi a jika sun kashe zuciyarsu, sun sace fanka a masallaci

Mustapha ya ce tabbas karfe daya na dare suka ji ana ta harbe-harbe inda aka kashe 'yan sanda biyu da farar hula daya.

Ya ce:

"Cikin dare misalin karfe daya muka ji ana ta bude wuta inda aka kashe jami'an 'yan sanda biyu da farar hula daya.
"Sannan an harbi wani farar hula daya inda yanzu haka ya na asibiti don karbar kulawa, har ila yau an sace mutane da dama."

Martanin 'yan sanda kan harin

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Abubakar Yazid ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai bai bayyana adadin mutanen ba.

Ya ce:

“Tabbas an kai hari a Kasuwar-Daji da safiyar yau, har yanzu bamu tabbatar da yawan mutanen da abin ya shafa ba.”

‘Yan daba sun farmaki kwamishina a Adamawa

Kun ji cewa, wasu ‘yan daba sun kai farmaki gidan kwamishinan Muhalli, Mohammed Sadiq a jihar Adamawa.

Sadiq ya gamu da tsautsayin ne a daren ranar Lahadi 11 ga watan Faburairu inda ya samu raunuka da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel