Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Daba Suka Farmaki Kwamishina a Jihar Arewa, Sun Sace Motarsa
- Yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar a jihar Adamawa, wasu ‘yan daba sun farmaki kwamishinan Muhalli a jihar
- Mohammed Sadiq ya gamu da tsautsayin ne a daren jiya Lahadi 11 ga watan Faburairu a gidansa da ke birnin Yola na jihar
- Rahotannin sun tabbatar da cewa kwamishinan ya samu raunuka wanda yanzu haka ya na asibiti mai zaman kansa a Yola
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Adamawa – Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai farmaki kan kwamishinan Muhalli a jihar Adamawa.
Maharan sun farmaki Mohammed Sadiq ne a daren jiya Lahadi 11 ga watan Faburairu tare da sace motar da yake hawa.

Asali: Facebook
Yadda 'yan daban suka farmaki kwamishinan
Bayan harin, rahotannin sun tabbatar da cewa kwamishinan ya samu raunuka wanda yanzu haka ya na asibiti mai zaman kansa a Yola.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da cewa maharan sun kai farmakin ne kan kwamishinan a gidansa da ke birnin Yola na jihar Adamawa.
Mataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa George Farauta da wasu jami’an gwamnati sun kai ziyara wurin kwamishinan da ke kwance a asibiti.
Gwamna Finitiri ya gargadi jama'a jihar
Farauta yayin ziyarar jajen, ta yi addu’ar neman lafiya ga kwamishinan da kuma kare faruwar hakan a gaba.
Wannan hari kan kwamishinan na zuwa ne bayan Gwamna Ahmadu Fintiri ya fitar da wata sanarwa kan shirin fasa rumbun abinci a jihar.
Gwamnan ya ce wasu mutane a jihar su na daukar nauyin bata gari don kawo rashin zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan
An ji kunya: Matasa masu karfi a jika sun kashe zuciyarsu, sun sace fanka a masallaci
Ana zargin hakan ne yayin da mutane ke cikin halin yunwa a kasar wanda hakan ka iya tunzura jama'a fasa rumbunan gwamnati.
A baya ma hakan ya taba faruwa a jihar inda mutane ke zargin an tara kayan abinci tun lokacin annobar 'Corona'.
DSS ta tsare Oscar a Abuja kan wani zargi
A baya, kun ji cewa hukumar tsaro ta DSS ta tsare Daraktan fina-finan Kannywood, Sunusi Oscar a Abuja.
Hukumar na zargin Oscar da furta wasu kalamai da suka shafi barazanar kisa ga wani jigo a gwamnatin Kano.
Asali: Legit.ng