'Yan Sanda Sun Samu Gagarumar Nasara Kan Masu Garkuwa da Mutane a Jihar Bauchi

'Yan Sanda Sun Samu Gagarumar Nasara Kan Masu Garkuwa da Mutane a Jihar Bauchi

  • An rage mugun iri na miyagu a jihar Bauchi bayan rundunar ƴan sandan jihar ta samu nasarar halaka masu garkuwa da mutane mutum biyar
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da hakan ya bayyana cewa an sheƙe miyagun ne a ƙaramar hukumar Giade ta jihar
  • Kwamishinan ya ce an samu nasarar ne tare da haɗin gwiwar tawagar mafarautan Ahmed Ali Kwara bayan an yi artabu da miyagun

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi -Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi tare da haɗin gwiwar tawagar mafarautan Ahmed Ali Kwara, sun yi nasarar kashe wasu mutum biyar da ake zargi da yin garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Giade ta jihar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jami'an tsaron sun kuma samu nasarar ƙwato bindigogi a hannun masu garkuwa da mutanen bayan artabun da suka yi.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Amarya ta hallaka mijinta a jihar Neja

'Yan sanda sun halaka masu garkuwa da mutane a Bauchi
'Yan Sanda sheke masu garkuwa da mutane a Bauchi Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Auwal Muhammad Musa ne ya bayyana haka a ranar Litinin, yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishin ƴan sanda na ƙaramar hukumar Giade, rahoton Nigerian Tribune ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishin ƴan sandan ya yi bayanin cewa jami'an tsaron sun samu nasarar halaka masu garkuwa da mutanen ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairun 2022

Yadda aka sheƙe masu garkuwa da mutanen

Ya yi bayanin cewa jami'an tsaron sun samu nasarar ne bayan samun bayanan cewa waɗanda ake zargin ɗauke da bindigu, sun shiga garin na Giade da nufin yin garkuwa da mutane.

Ya bayyana cewa bayan samun bayanan, jami'an tsaron tare da haɗin gwiwar tawagar mafarautan Ahmed Ali Kwara, sun yi gaggawar kai ɗauki tare da yin artabu da miyagun.

Kwamishinan ya yi nuni da cewa sakamakon artabun da aka yi da miyagun, ya sanya an halaka dukkan waɗanda ake zargin nan take.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun tare matafiya, sun tafka mummunar ɓarna a jihar APC

Musa ya bayyana cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wani Abdullahi, ne ya gayyato waɗanda ake daga jihohin Bauchi da Taraba.

Karanta wasu labaran kan garkuwa da mutane

Babban basarake ya bayyana yadda ya tsira daga hannun masu garkuwa da mutane

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

Ina sukar biyan da kudin fansa a baya, sai da aka sace ni na gane, tsohon shugaban DSS ya magantu

Ƴan Sanda Sun Farmaki Maɓoyar Masu Garkuwa da Mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, sun kai farmaki a maɓoyar wasu masu garkuwa da mutane.

Jami'an tsaron a yayin farmakin sun samu nasarar cafke mutum shida da ake zargi, waɗanda suka haɗa da maza huɗu da mata biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel