Wata Sabuwa: Amarya Ta Hallaka Mijinta a Jihar Neja

Wata Sabuwa: Amarya Ta Hallaka Mijinta a Jihar Neja

  • An shiga jimami da takaici a jihar Neja bayan wata sabuwar amarya ta aikata wani ɗanyen aiki kan mijinta na sunnah da aka ɗaura musu aure
  • Amaryar wacce ba ta cika wata biyu ba a ɗakin mijinta ta yanke shawarar salwantar da ransa ta hanyar ɗaba masa wuƙa
  • Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce ana cigaba da bincike don cafko amaryar wacce ta tsere

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Wata sabuwar amarya ƴar shekara 20 mai suna Aisha Aliyu da ke ƙauyen Nasarawa, a ƙaramar hukumar Lapai a jihar Neja ta kashe mijinta mai suna Idris Ahmadu.

Mazauna garin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Tsagerun ƴan bindiga sun kashe fitaccen lauya a Najeriya

Amarya ta halaka mijinta a Neja
Sabuwar amarya ta salwanta da ran mijinta a jihar Neja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Majiyoyi da yawa sun bayyana cewa ma'auratan sun yi aure ne a ranar 31 ga watan Disamban 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗaya daga cikin majiyoyin ya bayyana cewa ma’auratan sun ɗan samu ƴar rashin fahimta ne da yammacin ranar Lahadi, kuma an sasanta su kafin su kwanta, kwatsam cikin tsakar dare sai mahaifiyar marigayin ta ji yana kururuwa.

A kalamansa:

"Da mahaifiyar ta fito tare da sauran mazauna garin, sai suka gan shi a kwance cikin jini. Ya yi ƙoƙarin fita daga ɗakin amma ya faɗi a bakin ƙofa. Amma har ya zuwa yanzu, ba mu san inda matarsa ​​take ba."

Majiyar ya ce matar ta fara daɓawa mijin wuƙa ne a kirjinsa kafin daga bisani ta yanka shi.

Da aka tambayi ko auren dole ne, majiyoyi sun ce ma’auratan sun shafe shekaru suna soyayya amma kafin a sanya ranar ɗaurin auren amaryar ta sauya ra’ayi, sai dai daga baya an sasanta komai.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun tare matafiya, sun tafka mummunar ɓarna a jihar APC

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

"Yau 12/02/2024 (Litinin), da misalin ƙarfe 12:00 na dare, an samu labari cewa da sanyin safiya, wani Idris Ahmadu daga ƙauyen Nasarawa, a Lapai, matarsa, Aisha Aliyu, mai shekaru 19/20 a wannan adireshin ta daɓa masa wuka har lahira.
"Kafin isowar ƴan sanda a wurin, wacce ake zargin ta gudu zuwa wani wuri da ba a san ko ina ne ba, yayin da ake ci gaba da ƙoƙrin cafke wacce ake zargin, ana ci gaba da gudanar da bincike."

Miji Ya Halaka Matarsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ɗan Najeriya mazaunin ƙasar Burtaniya, ya halaka matarsa ta aure har lahira.

David Olubunmi Abodunde ya shiga hannun ƴan sanda bisa zargin laifin kashe matarsa, Taiwo Owoeye Abodunde, wata ma'aikaciyar jinya a Suffolk, Burtaniya

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel