Dalibin Shekarar Ƙarshe a Jami’ar AUA Ya Kashe Abokiyar Karatunsa Akan iPhone

Dalibin Shekarar Ƙarshe a Jami’ar AUA Ya Kashe Abokiyar Karatunsa Akan iPhone

  • Rundunar 'yan sanda ta ce ta kama wani dalibin ajin karshe a jami'ar Adekunle Ajasin, Akungba (AAUA) bisa zargin kashe abokiyar karatunsa
  • Rahoton 'yan sandan ya yi nuni da cewa dalibin mai suna Olubodun Sanni ya shiga har dakin kwanan dalibai ya kashe ta
  • An kama dalibin ne ta hanyar amfani da fasahar zamani aka bi diddigin wayar dalibar kirar iPhone da ya sace bayan ya kashe ta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Ondo - An kama wani matashi dan shekara 21 da ke karatu a jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba (AAUA) Olubodun Sanni, bisa zargin kashe wata Mis Adekunle Adebisi Ifeoluwa.

An tsinci gawar Miss Adekunle a ranar 2 ga Fabrairu, 2024 a cikin wani gida mai daki daya da ta yi haya a wajen makarantar, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Babban lamari ya faru bayan mata ta yi ajalin makwabciyarta da wuka kan wani dalili, an rasa ta cewa

Yan sanda sun kama dalibin da ya kashe abokiyar karatunsa
Yan sanda sun kama dalibin da ya kashe abokiyar karatunsa kuma ya tafi da wayarta kirar iPhone. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ta kasance dalibar aji 3 a sashen nazarin tattalin arziki, kuma an yi zargin Sanni da daba wa dalibar wuka har lahira tare da sace mata waya kirar iPhone XR.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ‘yan sandan Ondo, Abayomi Peter Oladipo, ya ce ‘yan sandan sun gano cewa wayar dalibar ta bata bayan kisan, Tribune Online ta ruwaito.

Abayomi ya bayyana cewa, ‘yan sanda ta hanyar amfani da fasahar zamani sun gano wayar a hannun wani dalibi mai suna Sanni wanda kuma makwabcin marigayiyar ne.

Ya ce: "Wayar da aka gano ta kai ga kara tsananta bincike kan wanda ake zargin wanda kuma ya amsa laifinsa tare da ba da cikakken bayani game da abin da ya faru."

Yan sanda sun kama matashi ya kashe abokinsa a Kogi

Ya ce za a gurfanar da Sanni gaban kotu a karshen binciken.

Kara karanta wannan

NNPP ta yadu zuwa wajen Kano, Jam’iyya Ta Samu ‘Dan Majalisa a Jihar Nasarawa

Abayomi ya kuma bayyana cewa rundunar ta kama wani Umar Ibrahim wanda ya kashe abokinsa, Mohammadu Adamu.

Umar ya kashe Adamu ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Ogali ta jihar Kogi.

A nasa bangaren, Umar ya ce ya kashe Adamu ne a lokacin da ya lura cewa Adamu da wani Basiru sun shirya yin garkuwa da shi don su kashe shi.

Yan bindiga sun halaka dan takarar majalisar tarayya

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa wani dan takarar majalisar tarayya na jam'iyyar PDP ya gamu da ajalinsa a hannun 'yan bindiga a Anambra.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun juma suna jin haushin dan siyasar kan yadda yake tsoma baki a ayyukan ta'addanci da suke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel