Babban Lamari Ya Faru Bayan Mata Ta Yi Ajalin Makwabciyarta da Wuka Kan Wani Dalili, an Rasa Ta Cewa

Babban Lamari Ya Faru Bayan Mata Ta Yi Ajalin Makwabciyarta da Wuka Kan Wani Dalili, an Rasa Ta Cewa

  • An shiga mummunan yanayi da tashin hankali bayan wata mata ta yi ajalin makwabciyarta a jihar Legas
  • Rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta ce ta yi nasarar cafke matar da ake zargi da kisan makwabciyarta a jihar
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Talata 13 ga watan Faburairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta yi nasarar cafke wata mata da zargin kisan makwabciyarta.

Wacce ake zargin mai suna Cynthia Aigbondon ana zarginta daba wa wata mai suna Barakar wuka bayan samun 'yar hatsaniya.

An cafke matar da ta hallaka makwabciyarta da wuka
Matar ta hallaka makwabciyarta ne da wuka. Hoto: NPF, Lagos State.
Asali: Facebook

Wace sanarwa rundunar 'yan sanda ta fitar?

Kara karanta wannan

An ji kunya: Matasa masu karfi a jika sun kashe zuciyarsu, sun sace fanka a masallaci

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Talata 13 ga watan Faburairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hundeyin ya ce mijin marigayiyar mai suna Lukmon Adio ya kai rahoto a ofishin 'yan sanda da ke Ajegunle a jihar, cewar TheCable.

Ya ce tuni aka dauki wacce tsautsayin ya fada kanta tare da kai ta asibiti inda aka tabbatar da cewa ta rasu.

Yadda lamarin ya faru a Legas

A cewarsa:

"Wata 'yar hatsaniya ta faru inda wacce ake zargin ta caka wa Barakat wuka a gefen kirjinta.
"An dauke ta zuwa asibiti yayin da likitoci suka tabbatar da cewa ta mutu."

Hundeyin ya ce an dauki gawar marigayiyar zuwa wurin adana gawarwaki a wani asibiti, kamar yadda Daily Post ta tattaro.

Ya ce rundunarsu ta isa wurin don neman shaidu da kuma daukar hotuna da za su taimaka wurin bincike.

Kara karanta wannan

Dalibar aji 4 a jami'ar Najeriya ta dauki ranta da kanta, an gano dalili

Wannan na zuwa ne kwana ɗaya kacal bayan wata amarya ta hallaka mijinta a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya wanda ba su dade da yin aure ba.

Yan saba sun farmaki kwamishina

Kun ji cewa, wasu da ake zargin 'yan saba ne sun farmaki kwamishinan Muhalli a jihar Adamawa, Mohammed Sadiq.

Mohamed ya hadu da tsautsayin ne a gidansa a daren ranar Lahadi 11 ga watan Faburairu a Yola.

Rahotanni sun tabbatar da cewa daga bisani an cafke wasu mutane hudu da zargin hannu a fashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel