Remi Tinubu: An Tsauraro Tsaro a Kano Kan Abu 1 Tak

Remi Tinubu: An Tsauraro Tsaro a Kano Kan Abu 1 Tak

  • Uwargidan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Remi Tinubu za ta kai ziyara birnin Kano domin ƙaddamar da wani aiki
  • Gwamnatin jihar Kano tare da rundunar ƴan sandan jihar sun sanar da ɗaukar tsauraran matakan tsaro saboda ziyarar uwargidan shugaban ƙasan
  • Gwamnatin jihar ta buƙaci mazauna birnin Kano da su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu domin tarbar Remi Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - A yau ne uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, za ta ziyarci jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa, ana sa ran Remi Tinubu za ta ƙaddamar da ginin tsangayar karatun lauyoyi da aka sanya sunanta a jami’ar Maryam Abacha da ke Kano.

Kara karanta wannan

Najeriya vs Cote d'Ivoire: Shugaba Tinubu ba zai halarci wasan karshe na AFCON ba, bayanai sun fito

Remi Tinubu za ta ziyarci Kano
An tsaurara tsaro a Kano kan ziyarar Remi Tinubu Hoto: Sen. Oluremi Tinubu, CON
Asali: Facebook

Da yake zantawa da manema labarai a Kano, Darakta Janar na yaɗa labarai na Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature, ya ce an samar da isassun tsare-tsare na tsaro domin tabbatar da nasarar ziyarar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane shiri gwamnatin Kano ta yi?

Ya ce gwamnatin jihar tare da ƴan sanda sun tsara yadda za a samar da tsari mai kyau kan yadda za a samar da tsaron da ake buƙata.

Bature ya ce gwamnatin jihar da hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don samar da yanayi mai kyau ga maziyartan.

Don haka gwamnati ta yi kira ga mazauna birnin da su gudanar da rayuwarsu cikin lumana, su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu domin tarbar uwargidan shugaban ƙasan.

Jaridar Gazettengr ta ruwaito kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Hussaini Gumel, a wata hira ta wayar tarho a ranar Asabar, yana cewa:

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta shiga sabuwar matsala kan tuhumar tsohon gwamna, bayanai sun fito

"Mun tattara isassun jami’an tsaro da za su bai wa uwargidan shugaban ƙasa kariya kafin, a lokacin, da kuma bayan ziyarar.
"Ba za mu yarda da duk wani aiki da zai iya kawo rudani kafin, a lokacin, da kuma bayan ziyarar ba."

"Sauƙi Na Nan Tafe" - Remi Tinubu

A wani labarin kuma kun ji cewa uwargidan shugaban ƙasa Tinubu, Remi Tinubu, ta kwantar da hankalin ƴan Najeriya kan halin ƙuncin da ake ciki.

Remi Tinubu ta bayyana cewa wannan halin ƙuncin na ɗan lokaci kuma sauƙi yana nan tafe nan bada daɗewa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel