Masu Garkuwa Da Mutane
Akalla mutane bakwai da suka hada da jarirai biyu da mata biyar ne dakarun sojoji na rundunar Hadarin Daji suka kubutar a yayin wani samame da suka kai dajin Zamfara
'Yan bindigan da suka yi garkuwa da dalibai a jihar Kaduna, sun aika da bujayarsunkan kudaden fansan da za a biya kafin yaran su shaki iskar 'yanci.
'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane akalla 61 a wani sabon hari da suka kai garin Buda da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna. Yan sanda ba su ce uffan ba.
Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta yi nasarar cafke wasu ƴan bindiga masu garkuwa da mutane waɗanda ta jima tana nemansu ruwa a jallo, sun shiga hannu.
Miyagun ƴan bindiga sun buƙaci yan uwan da mutanen da suka sace a Gonin Gora su haɗa Naira tiriliyan 40 a matsayin kuɗin fansa da kuma motoci da babura.
Masu garkuwa da mutane da suka sace almajirai a jihar Sakkwato sun nemi a tattara musu Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa gabanin su sako su.
A jihar Kano, jami’an NSCDC sun damke ‘dan shekara 85 da zargin garkuwa da mutane. Idan dai gaskiya ne, da alamu tsufa tayi wa wannan mutumi gardama.
Tsagerun 'yan bindiga sun kai farmaki Anguwar Makera karkashin garin Kwasakwasa da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna tare da kashe masallata.
Matar shugaban kasa Oluremi Tinubu ta yi Allah wadai da ‘yan bindiga, ta bayyana su a matsayin matsora kuma ta nemi a dunga yanke hukuncin kisa a kansu.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari