Dikko Radda: Gwamnan Katsina da Ya Ce Ba Zai Yi Sulhu da Ƴan Bindiga Ba

Dikko Radda: Gwamnan Katsina da Ya Ce Ba Zai Yi Sulhu da Ƴan Bindiga Ba

  • Gwamnan jihar Katsina, ya fadi dalilin da ya sa ya ƙi amincewa da shawarar mutane na yin sulhu da ƴan bindiga
  • Malam Umar Dikko Radda ya ce yin sulhun wata alama ce da ke nuna wa 'yan bindigar cewa sun fi ƙarfin gwamnati
  • Wani dan siyasa kuma mai sharhi kan lamuran yau da kullum a jihar, Alhaji Mati Bamba, ya ce matakin Gwamna Radda mace ce da ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Katsina - Malam Dikko Umaru Radda, gwamnan jihar Katsina, ya ce gwamnatinsa ba za ta nemi sulhu da ƴan bindiga a jihar ba.

Gwamna Dikko Radda ya yi magana akan matsalar tsaro
Katsina: Radda ya fadi matsayarsa kan yin sulhu da 'yan bindiga. Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Radda ya gana da tawagar ƴan jaridan Katsina

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Atiku ya caccaki Tinubu, ya fadi hanyar kawo karshen matsalar

A cewarsa, yin sulhu kamar yana buɗe kofar ɓaraka ne ga matsalar tsaro, domin ƴan bindiga za su ɗauka gwamnati ba ta da sauran kataɓus.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Radda wanda ya nuna goyon bayan kan kaddamar da ƴan sandan jihohi ya ce akwai bukatar gwamnoni su zama masu jan ragamar tsaro a jihohinsu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ofishinsa a ranar Laraba a lokacin da ya karbi baƙuncin wakilan kamfanin Media Trust Group, mamallakan jaridar Daily Trust.

"Illolin yin sulhu da ƴan bindiga" - Radda

Radda ya ce dokar hukumomin tsaro ba ta ba gwamnoni damar juya akalar jami'an tsaro ba, don haka dole a rika samun tasgaro a harkar.

"Wasu na ganin cewa hanya mafi sauki ta magance matsalolin tsaro ita ce zaman sulhu da 'yan bindiga, amma ni na ce ba zan taɓa yin hakan ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam Dikko da sojoji sun samu gagarumar nasara kan ƴan bindiga a watan Azumi

"Ai gwamnatin da ta shude a jihar ta yi zaman sulhu, amma a karshe me ya faru? Mun yi asarar kudin jama'a ne kawai muka ƙara masu ƙarfi."

- Dikko Radda.

Radda: "Mun yi alkawarin samar da tsaro"

Gwamnan ya kara da cewa:

"Mutane sun zabe mu saboda mun yi masu alkawarin dawo da zaman lafiya da tsaro, domin shi ne babban aiki da ya ke ciwa kowa tuwo a kwarya a Katsina.
"Hankalinka zai yi matukar tashi idan ka shiga garuruwan da aka kai wa farmaki, ga asarar rayuka da dukiya, ga lalata rayuwar mata da sauransu."

Radda ya ce abubuwan da ke faruwa a jihar ya sa ya dauki matakai na kashin kansa tunda ba shi da iko a kan jami'an tsaron tarayya.

Matakan tsaro da Gwamna Radda ya dauka

Gwamnan ya ce matakin farko da ya dauka shi ne daukar alkawarin yaki da 'yan bindiga ba tare da zaman sulhu ba, yana mai cewa gwamnatinsa ba ta gaza ba.

Kara karanta wannan

NEC: Gwamnoni 16 sun goyi bayan ƙirkiro ƴan sandan jihohi domin dawo da zaman lafiya

Wani rahoton Leadership ya ruwaito Radda na cewa ya dauki matakin kaddamar da rundunar tsaro ta jihar, wadda kwalliya ta fara biyan kudin sabulu kan ayyukan da take yi.

Ya ce rundunar tsaron sun yi kokari na fatattakar 'yan bindiga daga biranen jihar zuwa dazuzzuka, inda ya ce dama can ne fagen fafatawa.

"Matakin Radda mace ce da ciki" - Bamba

Alhaji Mati Bamba, ɗan siyasa kuma mai sharhi kan lamuran yau da kullum a jihar Katsina, ya ce matakin Gwamna Radda na ƙin yin sulhu da ƴan bindiga tamkar mace ce mai ciki.

A cewarsa, ƙin yin sulhu da su, zai jawo asarar rayuka ne kawai na wadanda ba su ji ba basu gani ba, sakamakon gwamnatin ba za ta iya hana ƴan bindigar kai hare-hare ba.

"Bai kamata da ma gwamnati ta yi sulhu da ƴan bindiga ba, wannan shi ne taken manyan ƙasashe irinsu Amurka. Ina ta tabbacin mai girma gwamna na so a kawo karshen ta'addanci a Katsina.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya kawo hanyar magance matsalar 'yan bindiga cikin sauki

"To sai dai kuma, su ƴan bindigar nan suna da makaman da suka fi na jami'an tsaron mu kyau. Kullum muna jin irin munanan hare-hare da suke kai wa ƙauyukan Katsina."

Alhaji Bamba ya ce yana fatan gwamnatin jihar Katsina, za ta ƙara dibar sabbin dakarun tsaron jihar tare da ba su makamai da za su iya yakar ƴan bindigar.

"Dakarun tsaro da gwamnan ya kaddamar suna aiki sosai, an samu sauki, amma kuma ƴan bindigar suma sun dauki sabbin salo na kai hare-haren, don haka akwai buƙatar canja matakai."

- A cewar Bamba.

Ramadan: Tsarin shirin ciyarwa a Katsina

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa Gwamna Dikko Radda ya fitar da N10bn domin aikwatar da shirin ciyarwa a watan Ramadana na bana.

Yayin kaddamar da kwamitin aiwatar da shirin, Radda ya ce matakin zai rage radadin tsadar rayuwa da al'umma ke fuskanta a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel