Dattawan Arewa Sun Faɗi Malamin Musulunci 1 da Suke Goyon Bayan Ya Tattauna da Ƴan Bindiga

Dattawan Arewa Sun Faɗi Malamin Musulunci 1 da Suke Goyon Bayan Ya Tattauna da Ƴan Bindiga

  • Dattawan Arewa sun buƙaci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinibu ya bai wa Sheikh Gumi damar tattauanawa da ƴan bindigan da suka sace ɗalibai a Kaduna
  • Kungiyar dattawan NEF ta bayyana goyon bayanta ga yunkurin Gumi na shiga tsakani da ceto ɗaliban cikin ƙoshin lafiya
  • Tun farko dai fitaccen malamin ya roƙi Tinubu ya ba shi dama, ka da ya yi kuskuren da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta goyi bayan shirin fitaccen malamin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, na tattaunawa da ‘yan bindigan da suka sace ɗalibai kusan 287 a Kaduna.

Idan baku manta ba Sheikh Gumi ya yi tayin cewa zai sadaukar da kansa wajen tattaunawa da ƴan bindiga domin ceto ɗalibai makarantar Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jero mutanen da suka koma yaƙarsa saboda matakan da ya ɗauka a Najeriya

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi.
NEF Ta Roki Bola Tinubu Ya Ba Gumi Damar Tattaunawa da Yan Bindiga Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta rahoto cewa ana ci gaba da samun karuwar rashin tsaro a yankin Arewa musamman a jihohin Kaduna da Borno a 'yan kwanakin nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’addan sun farmaki makarantar gwamnati ta Kuriga inda suka yi harbi kana suka tafi da dalibai da malaman makarantun.

A wani yunkuri na ganin an sako su, fitaccen malamin addinin musuluncin ya bukaci shugaba Bola Tinubu, ya ba shi damar tattaunawa da ‘yan fashin.

Ya kuma bukaci shugaban kasar da kada ya sake maimaita kuskuren da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi, wanda ya tsohe kunnensa game da batun tattaunawa da 'yan bindiga.

Manyan Arewa sun goyi bayan Gumi

Yayin wata hira ranar Asabar, kakakin NEF, Abdul-Azeez Suleiman, ya ce kamata ya yi a tallafa wa Sheikh Gumi "domin a kawo karshen rikicin Kaduna cikin lumana."

Kara karanta wannan

Shugabannin APC sun faɗawa Tinubu mataki 1 da ya kamata ya ɗauka kan wasu hafsoshin tsaro a Najeriya

A rahoton Ripples Nigeria, ya ce tattaunawa da ƴan binduga, "ba yana nufin halatta ayyukansu ko yafe musu bane, sai dai wani yunƙuri ne na shawo kan lamarin da ceto ɗaliban."

"Yayin da wasu ke tababar halascin zama da maharan, ya kamata a yi la'akari da fa'idojin da ke tattare da zaman tattaunawa. A kowane irin rikici, tattaunawar sulhu na da muhimmanci wajen samo mafita."
"Ta hanyar tattaunawa da su, Gumi zai iya fahimtar koke-kokensu da dalilansu, wanda hakan zai iya sa a sako yaran cikin ƙoshin lafiya.
"Bugu da kari, bude ƙofar sadarwa da ‘yan fashin na iya ba da damar magance matsalolin da ke damun su kamar talauci, rashin ilimi, da kuma wariya da ke jawo hare-haren da suke kai wa."

- Abdul-Azeez Suleiman.

A wani rahoton kuma Sheikh Ahmed Abubakar Gumi, ya yi magana kan kuskuren da gwamnatin tarayya ke yi wajen ceto ɗalibai 287 da malamansu da aka sace a jihar Kaduna.

Malamin addinin musuluncin ya yi nuni da cewa amfani da ƙarfin tuwo kan ƴan bindigan ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel