Dubu Ta Cika: An Kama Hatsabiban Masu Garkuwa da Mutane da Ake Nema Ruwa a Jallo a Arewa

Dubu Ta Cika: An Kama Hatsabiban Masu Garkuwa da Mutane da Ake Nema Ruwa a Jallo a Arewa

  • Ƴan sanda sun kama masu garkuwa da wasu mutane biyu da ake nema ruwa a jallo kan aikata miyagun laifuka a jihar Adamawa
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya ce jami'ai da haɗin guiwar mafarauta sun kama su ne bayan tattara bayanan sirri
  • Kwamishinan ƴan sanda ya yabawa jami'an tsaron bisa wannan nasara, kana ya ɓukaci su ƙara zage dantse kan dukkan masu aikata laifuffuka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Adamawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu hatsabiban masu garkuwa da mutane biyu da ake nema a jihar.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya fitar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nemi Naira tiriliyan 40 da abu 2 a matsayin kuɗin fansar mutane 16 a jihar Arewa

Yan sanda sun samu nasara a Adamawa.
Hatsabiban masu garkuwa sun shiga hannu a Adamawa Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Ya ce dakarun ƴan sanda sun kama waɗanda ake zargin ne ranar Lahadi, 10 ga watan Maris, 2024 yayin da suka kai samame tare da wasu mafarauta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton The Nation, kakakin ƴan sandan ya ce an kama su ne bayan samun bayanan sirri kan wurin da suke ɓuya a garin Ngurore da ke ƙaramar hukumar Yola ta Kudu.

An gano sunayen masu garkuwan da ƴan sanda suka kama

Ya bayyana sunayensu da, Ahmed Muhammad mai shekaru 37 kuma mazaunin karamar hukumar Song; da Muhammed Haruna mai shekaru 25 kuma mazaunin Jambutu, karamar hukumar Yola ta Arewa.

"An kama wadanda ake zargin ne bisa laifin yin garkuwa da Saddam Ahmadu ɗan garin Belel a karamar hukumar Maiha da Buba Adamu daga karamar hukumar Shani ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya maida zazzafan martani kan garkuwa da ɗalibai da ƴan gudun hijira a jihohi 2

"Sun karɓi maƙudan kuɗi da suka kai N4,700,000 a matsayin kuɗin fansa daga hannun ƴan uwan waɗanda suka yi garkuwa da su.
"Wani abin sha'awa, an samu nasarar kwato bindiga kirar AK-47 guda daya da harsashi 25 daga hannun wadanda ake zargin."

- Suleiman Nguroje.

CP ya jinjina wa jami'an tsaro

Kwamishinan ƴan sandan Adamawa, CP Dankombo Morris, ya nuna farin cikinsa bisa wannan nasara da jami'an tsaron suka samu, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Ya yaba wa Kwamandan tawagar Crack da mafarauta bisa dabarun aikin da suka yi amfani da su wajen samun nasara, sannan ya bukaci su ci gaba da haka.

Ƴan sanda za su tabbatar da tsaro a Ramadan

A wani rahoton kuma rundunar ƴan sanda ta aike da saƙon gaisuwa da taya murna ga Musulmin Najeriya yayin da suka fara azumtar watan Ramadan.

Sufetan ƴan sandan na kasa ya jaddada shirin rundunar na tabbatar da tsaro a lungu da saƙon Najeriya a wannan wata mai albarka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel