Zamfara: Sojojin Najeriya Sun Halaka Wani Shugaban Ƴan Bindiga da Mayakansa

Zamfara: Sojojin Najeriya Sun Halaka Wani Shugaban Ƴan Bindiga da Mayakansa

  • Sojin saman Najeriya sun samu nasarar halaka Kachallah Damina, wani hatsabibin shugaban ƴan bindiga da mayaƙansa a jihar Zamfara
  • Rahotan da Zagazola Makama ya fitar ya yi nuni da cewa akalla ƴan bindiga 50 tare da Damina ne sojojin suka kashe a harin bam ta sama
  • Kashe Damina a yanzu, ya jefa tsoro a zukatan ƴan bindiga da ke da sansanoni a dazuzzukan Zamfara, inda aka ruwaito sun fara tserewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Zamfara - Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa, harin da ta kai ta sama ya halaka shugaban ‘yan bindiga a jihar Zamfara, Kachallah Damina, da mayakansa da dama.

Rundunar ta kai farmakin ne biyo bayan bayanan da ta samu na wasu gungun ‘yan bindiga da suka yi yunkurin kai hari a kauyen Corner a karamar hukumar Bungudu a ranar 10 ga Maris, 2024.

Kara karanta wannan

DHQ ta fitar da cikakken jerin sunaye da hotunan dakarun sojojin da aka kashe a jihar PDP

Zamfara: Rundunar sojin saman Najeriya ta kashe Kachallah Damina
Kashe Damina ya jefa tsoro a zukatan ƴan bindiga, tare da tilasta su ne neman mafaka. Hoto: Nigerian Air Force
Asali: Twitter

Shahararren mai fashin baki kan harkokin tsaro a Arewa maso Gabas da yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makam, ya wallafa wannan bayanin a shafinsa na X a ranar 19 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makama ya ruwaito cewa a lokacin da aka kashe Damina, an gano yana fama da raunuka a jikinsa wanda ya same su a arangamarsa da dakarun Hadarin Daji a garin Dansadau.

Barnar da sojoji suka yi wa ƴan bindiga

Wata majiyar tsaro ta shaidawa Makama cewa, cikin babura 58 na 'yan bindiga da suka fita kai farmakin, babura 11 ne kawai suka dawo, da yawansu an kashe mahayansu.

"Sama da ƴan bindiga 50 ne aka halaka tare da lalata babura da dama. Wannan harin shi ne mafi girma da aka samu nasara akan 'yan bindigar.
"Sojojin Najeriya na ci gaba da farmakar shugabannin ƴan bindiga domin ganin sun kakkabe su."

Kara karanta wannan

Mataki mai karfi da hukumar soji ta dauka a Delta bayan kashe mata jami'ai 16

- A cewar majiyar.

Rashin imanin Damina da hare-harensa

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa Damina asalin dan karamar hukumar Kankara ne da ke jihar Katsina, wanda ya addabi jihohin Sokoto, Kebbi, Katsina da Zamfara.

Ya kasance yana kai mugayen hare-hare tare da yi wa mutane kisan gilla. Shi ne ɗan bindigar da ya zaro jariri daga cikin wata mata sannan ya kashe ta.

Damina ya na da babban sansaninsa a dajin Magami a wani waje da ke kusa da Kango, karkashin ikon Buharin Daji da Nagala.

Yadda Damina ya fara ta'addanci a Zamfara

Kashe Damina a halin yanzu, kamar yadda Makama ya bayyana, ya jefa tsoro a zukatan ƴan bindiga, tare da tilasta masu neman mafaka.

An ruwaito cewa Damina ya samu wannan aƙidar ta zama ɗan bindiga daga ayyukan ta'addancin da su Shehu Rekep da Alhaji Lawali Dumbulu suka yi a jihohin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Cushe a kasafin kudi: Sanata ya tabbatar da karbar Naira biliyan 1 na ayyukan mazaba

Wadannan shugabannin 'yan bindigar biyu, su ne suka fara harkar bindiga a Zamfara, Katsina, Sokoto da Kebbi, kuma suna da mayaka daga Mali da Burkina Faso wadanda ke hakar ma'adanai.

Karanta rahoton Makama a kasa:

Kisan sojoji 16: Matakin rundunar ta dauka

A wani labarin, rundunar soji ta tura wasu sababbin dakaru zuwa jihar Delta da Bayelsa domin fadada neman wadanda suka kashe sojoji 16 a garin Okuoma da ke jihar Delta.

Legit Hausa ta ruwaito cewa, rundunar ta kuma girke jiragen ruwa na yaki a gabar tekunan jihihin biyu yayin da ta sha alwashin kama wadanda suka aikata danyen aikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel